'Yan Boko Haram na horar da makiyaya tare da karbar shanu a matsayin haraji, Rahoto
- Sabon bincike ya nuna cewa 'yan ta'addan Boko Haram suna horar da makiyaya dabarun yaki
- An gano cewa 'yan ta'addan basu bar makiyayan ba, suna karbar harajin sa daya a cikin kowanne shanu 40
- Majiyar ta tabbatar da cewa wannan ya zama ruwan dare a wasu kauyukan Gonisaleri, Dawayya da Abari a Geidam
Kamar yadda SaharaReporters ta wallafa, makiyaya da 'yan Boko Haram sun kulla wata yarjejeniya mai tsari a wasu yankuna na jihar Yobe inda 'yan Boko Haram ke horar da makiyayan dabarun yaki.
SaharaReporters ta tabbatar da cewa wata majiya daga rundunar sojin Najeriya tace 'yan ta'addan na karbar sa daya a kowanne shanu 40 da sauran kayan abinci daga makiyayan a matsayin haraji.
An gano cewa, wasu daga cikin makiyayan da suka hada da kananan yara, ana basu makamai tare da horar dasu ta yadda za su gudanar da hari na gaba.
KU KARANTA: Bidiyon Dangote kai tsaye tare da ma'aikatansa yana kara karfafa musu guiwa
KU KARANTA: Kano: Dole 'yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara
"Horar da makiyaya da karbar haraji daga wurinsu ba yau aka fara ba a garin Geidam dake jihar Yobe. 'Yan ta'addan na bukatar abinci da suka hada da nama kuma suna horar da makiyaya a kauyukan Gonisaleri, Dawayya da Abari duk a karamar hukumar Geidam," majiya daga rundunar soji ta sanar.
"'Yan ta'addan na karbar sa daya a duk shanu 40 a matsayin haraji, suna bada hatimi tare da shaidar biya ga makiyaya. Abun tamkar a shirye ake yinsa," ya sake bayyanawa.
A wani labari na daban, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da abu mafi alheri da ya taba faruwa a Najeriya.
A yayin tattaunawa a shirin siyasarmu a yau wacce gidan talabijin na Channels yayi, gwamnan yace an samu manyan nasarori yayin mulkin.
Mai gabatarwa ya tambaya gwamnan ko ya sakankance da abinda takwaransa na APC yace, sai gwamnan yace: "Na yadda gaskiya, na amince dari bisa dari. Na san abinda na gada, na san matsalolin da na shiga. A wani lokaci na so tserewa. Amma da babu taimakon shugaban kasa Buhari, ba za mu daga kawunanmu a matsayin gwamnoni ba."
Asali: Legit.ng