Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki

Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki

- NNPC ta bayyana cewa karin farashin litar man fetur ba zai fara aiki ba sai ta kammala tattaunawa da kungiyar kwadago

- Babban manajan hulda da jama'a na NNPC, Kennie Obateru, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Juma'a

- A jiya ne babban manajan matatar, Mele Kyari, ya bayyana cewa NNPC ba zata cigaba da daukar nauyin tallafin man fetur ba

Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ta ce za a cigaba da siyar da man fetur a farashin da yake har sai ta kammala tattaunawa da kungiyar kwadago.

Kennie Obateru, babban manajan hulda da jama'a na NNPC, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a.

Wannan cigaban na zuwa bayan Mele Kyari, babban manajan kamfanin yace NNPC ba za ta iya jurewa cigaba da biyan tallafin man fetur ba.

KU KARANTA: Kano: Dole 'yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara

Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki
Da duminsa: NNPC ta bayyana lokacin da sabon farashin man fetur zai fara aiki
Asali: Original

KU KARANTA: Tsarikan makiyaya da kake fadi ba kamar kalmashe daloli bane, Miyetti Allah ga Ganduje

A yayin jawabi a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja, Kyari yace NNPC ba za ta iya jure cigaba da daukar dawainiyar biyan tallafin man fetur ba, don haka za a fara siyar dashi a farashinsa na kasuwa.

Kamar yadda The Cable ta wallafa, ya ce NNPC tana biyan N100-120 biliyan a kowanne wata domin barin farashin man fetur a yadda yake.

"Farashin zai iya zama tsakanin N211 da N234 na lita daya. Ma'anar shine masu siyan man fetur basu biyan farashin, wasu ke biyan musu," yace.

“A yau da muke magana, abinda matatar ke ciki shine ba za ta iya cigaba da daukar wannan dawainiyar ba."

A wani labari na daban, kungiyar gamayyar masana tsaro ta Najeriya (CCNSE) a ranar Laraba ta caccaki hafsoshin tsaron kasar nan da suka zabi su dinga aiki daga Abuja. Sun bukacesu da su koma yankin arewa maso gaba, tsakiyar inda rashin tsaro yafi kamari a kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta nuna damuwarta ta yadda watanni biyu da hawan sabbin hafsoshin tsaron amma koyaushe rashin tsaro kara kamari yake yi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Otedola Adekunle da sakataren kungiyar na kasa, Dr Chris Aklo, sun kalubalanci shugabannin tsaron da su tashi su tsaya kan nauyin da aka dora musu, ganin cewa watanni biyu sun isa a fara ganin alamun shawo kan matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel