Kyawawan hotunan bishiya mai shekaru 1400 dake fitar da ganye launin zinari

Kyawawan hotunan bishiya mai shekaru 1400 dake fitar da ganye launin zinari

- Wata budurwa ta baiwa jama'a abun magana bayan wallafa hotunan wata bishiya da tayi mai shekaru 1400

- Bishiyar tayi suna da yadda take zubar da ganyayyaki masu launin zinari wanda ke baiwa manyan kogi kala

- Jama'a ba su iya tsayawa kallo ba kadai, sun dinga fatan samun damar taba wannan bishiya mai matukar kyau

Wata ma'aboci amfani da kafar sada zumunta ta Twitter ta bayyana hotunan wata bishiyar Ginkgo mai matukar kyau.

Budurwar mai amfani da suna @avayonce, ta rubuta: "Ina ta tunanin wannan bishiyar ginkpo mai shekaru 1400."

KU KARANTA: Muna matukar jin kunyar yadda ake sace dalibai a kasar nan, Fadar shugaban kasa

Kyawawan hotunan bishiya mai shekaru 1400 dake fitar da 'ya'yan 'zinari'
Kyawawan hotunan bishiya mai shekaru 1400 dake fitar da 'ya'yan 'zinari'. Hoto daga Independent.co.uk
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: Dole 'yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara

Bishiyar Ginkgo tayi shekaru 1400 kuma tana zubar da ganyayyaki masu launin zinari, hakan yasa kalar ke matukar kayatarwa bayan sun fadi a kusa da bishiyar.

Wallafarta ta ja martani dubu dari uku da saba'in a yayin rubuta wannan rahoton.

@ThotVegan tace: "Tsabar kyau, babu shakka, shiyasa jama'a suka fara amfani da sunan bishiyoyi."

@_MEGA_MONK_ cewa yayi: "Duba wannan katuwar kyakyawar bishiyar. Zai yi kyau idan mutum ya dasa daya daga cikin rassanta. Zai samu abun tarihi."

@ah_nice_paprika yace: "A duk lokacin da na ganta, tana tuna min wata bishiyar duniyar katoon na tinkerr bell ne. Tana da matukar kyau."

Ana kiran bishiyar da bishiyar ginkgo ko kuma maidenhair kuma an shukata ne tun zamanin masarautar Tang a China (618-907), jaridar Daily Mail ta wallafa.

Tana nan wurin bangon Gua Guanyin dake yankin tsaunin Zhongnan a China. Ta kasance wurin da ke baiwa dubban masu yawon bude ido masauki.

A wani labari na daban, shugaban kasa M,uhammadu Buhari yace ta'addanci, mayar da jama'a 'yan gudun hijira da sauyin yanayi manyan kalubale ne ga jama'a da alakar dake tsakaninsu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce akwai matukar amfani kasashen duniya su yi aiki tare domin samo hanyoyin da ya dace wurin shawo kan wadannan kalubalen.

Ya sanar da hakan ne yayin jawabi a wani shagalin karbar wasikar jinjina a gidan gwamnati dake Abuja, inda yace wannan kalubalen manyan matsaloli ne ga al'umma. Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng