‘Yan Majalisa sun amince a gina wata Jami’ar Tarayya a Garin Shugaban kasa

‘Yan Majalisa sun amince a gina wata Jami’ar Tarayya a Garin Shugaban kasa

- Majalisar Wakilan Tarayya ta yarda a kafa sabuwar Jami’a a jihar Katsina

- Wannan jami’ar da za a kafa a Funtua za ta rika koyar da ilmin aikin gona

- Jami’ar za ta taimakawa yankin Funtua da ke kukan karancin makarantu

Majalisar wakilan tarayya ta amince da kudirin kafa jami’ar koyar da aikin gona a garin Funtua, jihar Katsina.

A makon da ya gabata ne majalisar wakilai ta bi sahun takwararta watau majalisar dattawa game da kafa jami’ar tarayyar a Funtua.

Katsina Post ta samu labari cewa tun a ranar Laraba, 17 ga watan Maris, 2021, ‘yan majalisar wakilai su ka yi na’am da kudirin.

KU KARANTA: Idan Bello ya yi Shugaban kasa, za a ga Ministoci ‘Yan shekara 27 - Obasanjo

Jaridar ta ce bayan an samu goyon-bayan majalisar wakilai, abin da ya rage shi ne shugaban kasa ya sa hannu a wannan sabon kudiri.

Da zarar shugaban kasa ya amince, ginin sabuwar jami’ar a jihar ta Katsina ta zama dokar kasa.

Idan aka kafa jami’ar tarayya ta aikin gona a Funtua, za ta zama babbar jami’ar da ake da ita a yankin kudancin Katsina na Karaduwa.

Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu a majalisar dattawa, Bello Mandiya shi ne wanda ya fara gabatar da wannan kudiri a majalisar tarayya.

KU KARANTA: Majalisar jihar Borno ta ce babu shirin tsige Gwamna Zulum daga ofis

‘Yan Majalisa sun amince a gina wata Jami’ar Tarayya a Garin Shugaban kasa
‘Yan Majalisar Wakilai Hoto: @Housengr
Source: Twitter

An dade ana kukan cewa akwai karancin manyan makarantu a yankin na kudancin jihar. Katsina

Makarantun koyan aikin malanta, jami’o’i da makarantun koyon aikin da su ke jihar Katsina sun taru ne a Daura, Dutsinma, da Katsina.

A kaf yankin Funtua, babu babbar makaranta sai makarantar koyon aikin ungonzoma da ke garin Malumfashi wanda ke bada shaidar satifiket.

Kwanaki aka ji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya na cewa za a kammala ginin jami’ar sufuri ta tarayya da ke Daura a watan Satumban 2021.

Amaechi ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar ganin aikin da ake yi domin tabbatar da cewa wadanda aka ba aikin su na abin da ya dace.

Source: Legit

Online view pixel