Tashin Hankali! Yan sanda Sun cafke Mambobin IPOB 16 da bindigu da Bama-Bamai

Tashin Hankali! Yan sanda Sun cafke Mambobin IPOB 16 da bindigu da Bama-Bamai

- Wasu da ake zargin mambobin IPoB ne dake da hannu wajen ta'addanci a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun faɗa komai hukunar yan sand

- Rundunar Yan sanda ta bayyana cewa waɗan da aka kama ɗin nada hannu a kisan da ake yima jami'an tsaro da kuma wasu ta'addanci a yankin

- Yan sandan sun kuma ce suɓ kwato makamai masu hatsari daga mambobin IPOB ɗin da suka cafke.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta cafke mambobin ƙunguyar dake ikirarin kafa ƙasar biyafara IPOB 16 da kuma kwato bindigu da bama-bamai a hannunsu.

KARANTA ANAN: Rundunar sojin hadin guiwa ta MNJTF za su iya kawo karshen Boko Haram, Idris Deby

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai magana da yawun rundunar, Frank Mba, ya fitar a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hukumar yan sandan ta zargi waɗan da aka kama ɗin da haɗa baki wajen tada rikice-rikice da kuma kai hari ga jami'an tsaro da kayayyakinsu a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ma wasu sassan ƙasar nan.

Legit.ng ta gano cewa an sami wannan nasarar ne bayan aikin haɗin guiwa tsakanin yan sanda, sojojin ƙasa, da sojojin sama domin kamo mutanen da ke da alhakin kai ma jami'an tsaro hari da kuma bata wurare da kayayyakin jami'an.

Waɗan da aka kama sun haɗa da; Ugochukwu Samuel, ɗan shekara 28 daga karamar hukumar Arochukwu Jihar Abia; Raphael Idang, ɗan shekara 31 ɗan karamar hukumar Odukpani jihar Cross River.

Tashin Hankali! Yan sanda Sun cafke Mambobin IPOB 16 da bindigu da Bama-Bamai
Tashin Hankali! Yan sanda Sun cafke Mambobin IPOB 16 da bindigu da Bama-Bamai Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sauran sun haɗa da Cletus Nwachukwu Egole, ɗan kimanin shekara 60, ɗan garin Orlu jihar Imo; da kuma Michael Uba, shima ɗan jihar ta Imo.

KARANTA ANAN: APC zata shigar da ƙarar Hukumar zaɓe da PDP kan saka jam'iyyar cikin Zaɓe a Jihar Sokoto

Sai dai ba'a bayyana sauran mutum 12 ba.

'Yan sandan sun bayyana cewa, binciken da suka gunar ya nuna mutanen na da hannu a mafi yawancin tashin hankullan da aka yi a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan.

"An kama waɗan da ake zargin a sassa daban-daban na ƙasar nan bayan juriya, da kuma saka fasaha a aikin." A cewar mai magana da yawun yan sandan.

Hukumar ta kuma ƙara da cewa, dukkan su za'a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.

A wani labarin kuma Buhari ya bukaci shugabanni da su zama nagari abin koyi ga al'umma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci shugabanni a dukkan matakai da su zama jagorori na gari

Shugaban ya kuma jaddada bukatarsa ga masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalolin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262