Gobara ta Laƙume ɗinbin dukiyoyi na maƙudan Kuɗaɗe a Kasuwar Gashua, Jihar Yobe

Gobara ta Laƙume ɗinbin dukiyoyi na maƙudan Kuɗaɗe a Kasuwar Gashua, Jihar Yobe

- Wata mummunar gobara ta ƙona dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a kasuwar Gashua, dake jihar Yobe, arewa maso gabashin ƙasar nan

- Shaidun da lamarin ya faru a idon su sun bayyana cewa wutar ta ɗaɗe tana ɓarna a kasuwar, tun daren Asabar har wayewar garin Lahadi.

- Mutane da yawa dake kasuwanci a kasuwar sun rasa dukiya mai ɗinbin yawa, kuma sunyi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da su taimake su

Dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe sun salwanta a wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Gashua, dake Jihar Yobe, Arewa maso gabashin Najeria.

ƘARANTA ANAN: Rundunar sojin hadin guiwa ta MNJTF za su iya kawo karshen Boko Haram, Idris Deby

Wasu shaidun gani da ido sun shaida ma jaridar Daily Trust cewa, gobarar wadda ta fara tun ran Asabar da dare ta cigaba da ɓarna har safiyar Lahadi.

Ɗaya daga cikin 'yan kasuwan dake gudanar da kasuwancin su a wajen, Alhaji Ibrahim Faraja, ya bayyana cewa dukiyoyi daban-daban sun ƙone a gobarar.

Ya ce an yi asarar abubuwa da yawa kamar, siminti, abincin dabbobi, kayan abinci, injina, da dai sauran makamantan su, waɗan da ake hada-hadar su a kasuwar.

Alhaji Ibrahim ya ce shi kansa ya yi asarar siminti na kimanin miliyan uku a gobarar.

Gobara ta Laƙume ɗinbin dukiyoyi na maƙudan Kuɗaɗe a Kasuwar Gashua, Jihar Yobe
Gobara ta Laƙume ɗinbin dukiyoyi na maƙudan Kuɗaɗe a Kasuwar Gashua, Jihar Yobe Hoto: @Fedfireng
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Atiku: Domin ceton kanmu, dole ne mu taimakawa gwamnatin Buhari

Ya kuma ƙara da cewa, duk da har yanzin ba'a tabbatar da musabbabin tashin wutar ba, mazauna garin na zargin asalin gobarar daga 'yan shaye-shaye ne dake zama a ƙasuwar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da su taimaka ma yan kasuwar da abun ya shafa.

Lamarin ya faru ne ƙasa da sati ɗaya bayan shaguna da yawa sun ƙone daga wata gobara da ta ɓarke a jihar Kastina.

A wani labarin kuma 'Yan fashin da suka sace mambobin RCCG sun nemi a biya 50 Miliyan

Yan fashin da suka sace mambobin ƙungiyar addinin kirista RCCG a Kaduna sun nemi a biya su 50 miliyan kuɗin fansa kafin su sake su

Mai magana da yawun RCCG a jihar Kaduna Alao Joseph ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan masu garkuwan sun tuntuɓe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: