Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya aikewa shugaba Buhari goron gayyata

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya aikewa shugaba Buhari goron gayyata

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya gayyaci shugaba Muhammadu Buhari taron sauyin yanayi da za'a gudanar ta yanar gizo a watan Afrilu.

An gayyaci Buhari ne tare da wasu shugabannin kasashe 39 a duniya, rahoton TheCable..

Fadar White House a ranar Juma'a ta saki jawabin cewa wannan ganawa da za'ayi zai tattauna muhimmancin lurra da sauyin yanayi da amfanin mayar da hankali kan lamarin ga tattalin arziki.

"A yau, shugaba Biden ya gayyaci shugabannin kasashe 40 kan sauyin yanayi da za'ayi ranar 22 da 23 ga Afrilu. Za'a haskawa duniya wannan taro na yanar gizo ga kowa ya gani," jawabin yace.

Bayan hawa a mulki a Junairu, Biden ya sanar da cewa zai gudanar da wannan taro domin janyo hankalin manyan kasashe wajen magance matsalar sauyin yanayi.

Hakan ya biyo bayan komawar Amurka yarjejeniyar Paris bayan Donald Trump yayi watsi da ita lokacin da yake kan mulki.

KU KARANTA: Kawai a kasheta, Mahaifin Amaryar da Kishiyarta ta bankawa wuta ya bukaci hukuma

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya aikewa shugaba Buhari goron gayyata
Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya aikewa shugaba Buhari goron gayyata
Asali: Twitter

KU DUBA: Ba ni ya taya ba, Ministan Buhari ya nisanta kansa daga Baturen zaben da aka jefa kurkuku kan taya APC magudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel