Shugabannin majalisun dokokin Arewa mao yamma sun yi alkawarin goyon bayan Tinubu a 2023

Shugabannin majalisun dokokin Arewa mao yamma sun yi alkawarin goyon bayan Tinubu a 2023

- Yayinda ake shirin murnar ranar haihuwarsa, Tinubu na cigaba da samun goyon baya

- Tun yanzu, an fara shirye-shiryen takaran zaben shugaban kasa a 2023

- Ana hasashen cewa mulki zao koma kudu bayan Buhari

Shugabannin majalisun dokokin Arewa maso yammacin Najeriya sun mara goyon bayansu ga jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, don takaran kujeran shugaban kasa a 2023.

Kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya bayyana hakan.

A jawabin da ofishin yada labaran Kakakin ya saki ranar Asabar, ya ce dukkan shugabannin majalisun sun bayyana goyon bayansu ne ranar Juma'a a jihar Kano.

A cewar jawabin, tsohon Kakakin majalisar jihar Kano, Abdullahi Yanshana, "kashi 95% na kuri'un jihar Kano a 2023 jagoran APC (Tinubu) za'a kadawa,"

Obasa ya ce dukkan shugabannin majalisun dake ci yanzu da kuma na baya a Arewa maso yamma sun alanta goyon bayansu ga Tinubu don ya gaji shugaba Buhari a 2023.

KU KARANTA: Kwana 2 bayan gyara wutan Maiduguri, yan Boko Haram sun sake lalatawa

Shugabannin majalisun dokokin Arewa mao yamma sun yi alkawarin goyon bayan Tinubu a 2023
Shugabannin majalisun dokokin Arewa mao yamma sun yi alkawarin goyon bayan Tinubu a 2023
Asali: Twitter

Kawo yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai bayyana niyyar takara a zaben 2023 ba.

Amma yadda makusantansa da masoyansa ke nema masa goyon baya, da alamun nan ba da dadewa ba zai alanta niyyarsa.

A ranar Asabar, Tinubu ya jagorancin lakcan Arewa House karo na 11 da ya gudana a jihar Kaduna.

KU DUBA: Zanga-zanga kan rashin makamai: Gwamnatin Buhari na shirin sayan sabbin makamai, cewar Hukumar Soji

A bangare guda, bayan ce-ce-ku-ce da aka shafe watanni ana yi game da kudirinsa na shugabancin kasa a 2023, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce zai tsallaka gadar idan ya isa wurin.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa gwamnan yace babu wani dan siyasa na gaske da zai yi watsi da damar zama shugaban kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel