Zanga-zanga kan rashin makamai: Gwamnatin Buhari na shirin sayan sabbin makamai, cewar Hukumar Soji

Zanga-zanga kan rashin makamai: Gwamnatin Buhari na shirin sayan sabbin makamai, cewar Hukumar Soji

- Kwana daya bayan rahoton zanga-zanga, hukumar Soji ta yi magana

- Hukumar Soji ta karyata cewa akwai jami'anta dake bin kudin alawus

- Wannan ba shi ne karo na farko da za'a samu labarin Sojoji sun bijirewa shugabanninsu ba

Hukumar Soji ta yi watsi da rahotannin cewa wasu jami'an Sojojin rundunar Operation Lafiya Dole sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai da kudin alawus a Maiduguri, birnin jihar Borno.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Mohammed Yerima, ya bayyana hakan a jawabi ranar Juma'a inda yace labaran da gidajen jarida suka yada ba gaskiyan abinda ya faru bane.

Ya ce kawai korafi wasu Sojojin rundunar MST suka yi bayan turasu yaki karkashin rundunar 'Exercise Tura Takaibango'.

A cewarsa, "misalin karfe 3 na ranar 25 ga Maris, wasu Sojojin rundunar MST 10 da 11 da aka tura atisayen Exercise Tura Takaibango karo na biyu a Bama suka yi wasu korafe-korafe."

"Amma ba tare da bata lokaci be aka magance matsalar kuma aka turasu faggen fama."

"Hakazalika akan lamarin rashin makamai kamar da kafafen yada labarai suka yada, matsayar Hedkwatar Soji itace kowani Soja na da hakkin tambayan makaman da suka dace don fita yaki."

"Gwamnatin tarayya na iyakan kokarinta wajen samar da isassun makamai don hadawa da wadanda ake amfani da su yanzu."

KU KARANTA: Ba ni ya taya ba, Ministan Buhari ya nisanta kansa daga Baturen zaben da aka jefa kurkuku kan taya APC magudi

Zanga-zanga kan rashin makamai: Gwamnatin Buhari na shirin sayan sabbin makamai, cewar Hukumar Soji
Zanga-zanga kan rashin makamai: Gwamnatin Buhari na shirin sayan sabbin makamai, cewar Hukumar Soji Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

DUBA NAN: 2023: Dalilin da yasa muka bari tsohon Shugaban hafsan soji ya dawo cikinmu, APC ta magantu

Jiya mun kawo muku cewa Sojojin rundunar Operation Lafiya Dole sun gudanar da zanga-zanga kan turasu faggen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram.

A cewar majiyoyi daga barikin Maimalari, Sojojin sun mamaye hedkwatar Operation Lafiya Dole ne a daren Alhamis suna harbin bindiga sama.

Sun bayyana cewa suna zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu alawus da kuma rashin isassun makaman yaki.

Za ku tuna cewa mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta'addan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel