Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai

Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai

- Wasu jami'an Soji dake faggen yaki sun yi wa kwamdandojinsu tawaye

- An sakaye sunayen Sojojin don gudun tsangwama da cin zarafi

- Sojojin sun yi alhinin yadda abokan aikinsu ke hallaka saboda rashin isassun makamai

Sojojin rundunar Operation Lafiya Dole sun gudanar da zanga-zanga kan turasu faggen yaki da 'yan ta'addan Boko Haram.

A cewar majiyoyi daga barikin Maimalari, Sojojin sun mamaye hedkwatar Operation Lafiya Dole ne a daren Alhamis suna harbin bindiga sama.

Sun bayyana cewa suna zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu alawus da kuma rashin isassun makaman yaki.

A jawabin wasu daga cikin sojojin da suka bukaci a sakaye sunayensu, sun bayyana yadda yan ta'addan Boko Haram suka hallaka Sojoji a harin Marte saboda makaman yan ta'addan sun fi nasu.

Channels TV ta bayyana cewa kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Isa Ado, ya tabbatar da labarin.

Wannan zanga-zanga na Soji ya biyo bayan fallasan da NSA Babagana Munguno yayi cewa an nemi kudin makamai an rasa karkashin tsaffin hafsoshin tsaro.

DUBA NAN: Janar Buratai ya karyata rahoton cewa ya ci kudin makamai

Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai
Rundunar Sojin Najeriya sun yi zanga-zanga kan rashin isassun makamai

DUBA NAN: Sabbin jiragen yaki, Super Tucano, guda 6 zasu iso a watan Yuli, Fadar shugaban kasa

Mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta'addan Boko Haram.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma'a, 12 ga Maris.

Amma mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma'a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng