Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa
- Gwamnatin shugaba Buhari ta bankado wani sabon zargin almundahanan kudin makamai
- Mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya ce wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro sun bace
- Monguni ya lashi takobin cewa gwamnatin Buhari za ta gudanar da bincike kan abinda ya faru
Mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.
A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta'addan Boko Haram.
NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma'a, 12 ga Maris.
Monguno ya kara da cewa sabbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada kwanakin baya basu ga kudaden ba, hakazalika basu ga makaman da aka ce a saya da su ba.
''Babu wanda ya san abin da aka yi da wadannan kudaden, amma da yardar Allah shugaban kasa zai bincika domin a gano inda aka kai su ko kuma a ina kayan suka shiga,'' in ji Monguno.
''Tun da dai ba a yi wani binciken kwarai ba, ba zan ce wani abu ba, amma dai kudi dai tabbas sun salwanta, kayan dai ba a gani ba, kuma sabbin shugabannin tsaro sun ce su fa ba su ga kayayyakin tsaro da ake magana ba a kai.''
"Ƙila wasu suna kan hanya daga Amurka, daga Ingila ko daga wasu wurare, amma yanzu a kasa ban gani ba su ma ba su gani ba,'' ya kara.
KU KARANTA: Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna
KU DUBA: Gwamna Zulum ya dauki nauyin karatun 'ya'yan talakawa, 'yan mata 800
Tsaffin hafososhin tsaron sune Janar Abayomi Olonisakin; Lt-Gen. Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; Air Marshal Sadique Abubakar, dukka maus murabus.
Bayan nada su tun shekarar 2015, Buhari ya sallami Buratai, Olonisakin, Ibas da Abubakar a Junairun 2021.
Bayan haka ya basu mukaman jakadu na musamman.
A wani labarin kuwa, fadar shugaban kasa ta fito ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya sake jaddada umarninsa na ganin bayan manyan masu laifi, wadanda su ka addabi Najeriya.
A ranar Alhamis, 11 ga watan Maris, 2020, shugaban kasar ya kara tabbatar da cewa jami’an tsaro su harbe duk wani wanda aka samu dauke da bindigar AK-47.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng