Ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin Buhari ba, Garba Shehu

Ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin Buhari ba, Garba Shehu

- Garba Shehu ya yi tsokaci kan jawabin NSA Manjo Janar Babagana Monguno

- Shehu ya rantse babu yadda za'ayi a saci kudin makamai karkashin Buhari

- Buratai ya kare kansa kan zargin da ake masa

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.

Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma'a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su.

Ya bayyana hakan ne yayin tsokaci kan kalaman mai baiwa kasa shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno.

Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka baiwa tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

NSA Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma'a, 12 ga Maris.

Tuni Monguno ya ce anyi masa mumunan fassara ne ba haka yake nufi ba.

Garba yace: "Kana magana kan kudi $1 billion da aka dauka daga cikin asusun rarar man fetur da izinin gwamnoni domin sayen makamai. Ina tabbatar muku cewa ko sisi bai bace ba cikin kudin."

"Rahotannin da ake yi a hirar da NSA yayi da BBC Hausa, ina ganin an yi masa mumunan fassara."

"NSA yayi maganganu biyu. Daya shine babu isassun makamai kuma wannan gaskiyane, na biyu shine ba'a gama siyayya ba."

"Har yanzu ana kan saye; ba abun da za'a saya a kasuwa bane. NSA bai yi zargin almundahana ba, saboda babu wani almundahana cikin wannan lamari."

KU KARANTA: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

Ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin Buhari ba, Garba Shehu
Ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin Buhari ba, Garba Shehu Credit: Presidency
Asali: UGC

Kun ji cewa Laftanan Janar Tukur Buratai, ya karyata rahoton cewa ya ci kudin da aka bada don sayan makamai lokacin da yake mulki.

Buratai wanda yayi murabus makonnin baya, ya bayyana hakan ta bakin lauyansa, Osuagwu Ugochukwu, ranar Juma'a.

Buratai ya bayyana cewa ko sau guda Monguno bai ambaci sunansa ba.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel