Kwararru ga hafsoshin tsaro: Ku koma arewa maso gabas na wata 6
- Kungiyar masana tsaro ta CCNSE ta caccaki hafsoshin tsaron Najeriya da suka zabi yin aiki daga Abuja
- Kamar yadda kungiyar ta bukata, shugabannin tsaron su tattara komtsansu su koma yankin arewa maso gabas
- Kungiyar ta koka da yadda rashin tsaron kasar nan ke kara gaba tun bayan sabon nadin a maimakon ya samu daidaituwa
Kungiyar gamayyar masana tsaro ta Najeriya (CCNSE) a ranar Laraba ta caccaki hafsoshin tsaron kasar nan da suka zabi su dinga aiki daga Abuja. Sun bukacesu da su koma yankin arewa maso gaba, tsakiyar inda rashin tsaro yafi kamari a kasar nan.
Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta nuna damuwarta ta yadda watanni biyu da hawan sabbin hafsoshin tsaron amma koyaushe rashin tsaro kara kamari yake yi.
Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Otedola Adekunle da sakataren kungiyar na kasa, Dr Chris Aklo, sun kalubalanci shugabannin tsaron da su tashi su tsaya kan nauyin da aka dora musu, ganin cewa watanni biyu sun isa a fara ganin alamun shawo kan matsalar tsaro.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu
KU KARANTA: Muna nan zuwa kanku, Shugaban sojin Najeriya ga Igboho da Dokubo
"Tun bayan da aka nada su a ranar 26 ga watan Janairun 2021, mun tsammaci cewa zuwa yanzu mun ga alamun garabawul a tsaron kasar nan. Amma abun takaici shine yadda rashin tsaron ke cigaba da tsananta," suka ce.
Sun koka da yadda dalibai 39 na kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi na Kaduna tare da wasu suke hannun 'yan bindigan.
"A madadin ganin sauyi, abinda har yanzu muke ji sune alkawarurruka. Wannan ba zai yuwu ba. Ba shine 'yan Najeriya ke tsammani ba. Muna son mu ga aiki da kuma yadda ake maganin wadannan miyagun.
“Shugaban kasa Buhari ya bada makonni shida daga ranar da aka yi bikin nada su a kan yana son ganin canji. Amma a gaskiya komai tsananta yake yi. 'Yan Najerya sun gaji kuma muna son ganin sakamakon da gagggawa."
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar APC, Badaru Abubakar, yace za a yi gagarumin taron jami'iyyar a watan Yuni.
Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai rade-radin dake yawo na cewa za a kara wa'adin mulkin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar kuma za a kara lokacin taron ya wuce watan Yuni.
Amma a wata tattaunawa da manema labarai a sakateriyar jam'iyyar APC da yayi a ranar Talata, Badaru yace kwamitin rikon kwaryan ya shirya domin sauke nauyin dake kansu.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng