Hakeem Baba-Ahmed: Dabaru Sun Ƙarewa Gwamnatin Buhari, Kullum Sai Bada Uzuri

Hakeem Baba-Ahmed: Dabaru Sun Ƙarewa Gwamnatin Buhari, Kullum Sai Bada Uzuri

- Mai magana da yawun kungiyar, NEF, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya ce dabaru sun kare wa fadar shugaban kasa

- Baba-Ahmed ya ce takaici ke kama shi jin yadda a kullum fadar shugaban kasar ke naman bada uzuri a maimakon magance matsalar tsaro

- Kakakin na NEF ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan kalaman Garba Shehu mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari

Hakeem Baba-Ahmed, Mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa, NEF, ya ce ya gamsu da cewa dabaru sun kare wa fadar shugaban kasa, The Cable ta ruwaito.

Baba Ahmed ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a Channel Television a ranar Juma'a.

Baba-Ahmed: Dabaru Sun Ƙarewa Fadar Shugaban Ƙasa, Kullum Sai Bada Uzuri
Baba-Ahmed: Dabaru Sun Ƙarewa Fadar Shugaban Ƙasa, Kullum Sai Bada Uzuri. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zulum Ya Ce Ya Kamata Mulkin Nigeria Ya Koma Kudu a 2023

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa yayin tattaunawar da aka yi da shi ya ce jam'iyyar adawa na amfani da kallubalen da kasar ke ciki wurin sukar gwamnati.

Ya ce wasu wadanda basu yi wa kasar fata nagari ne ke daukan nauyin tsirarun mutane da ke neman ballewa daga Nigeria domin ganin shugaban kasa ya yi kuskure.

A martaninsa, Baba-Ahmed ya ce yanayin da Shehu ke magana na jefa shi cikin damuwa kuma yana tunanin dabaru sun kare wa fadar shugaban kasar.

Kakakin na NEF ya ce yan Nigeria na son ganin an kawo karshen garkuwa da mutane ne ba wai bada uzuri ba.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutum 9 a Ƙananan Hukumomin Giwa da Birnin Gwari a Kaduna

Ya ce garkuwar ta bunkasa a karkashin gwamnatin Buhari kuma babu yadda zai musanta hakan duba da irin makaman da yan bindigan suka mallaka a yanzu.

"Idan suna fuskantar babbar kallubale, sai su yi ta zagaye suna kame-kame na bada uzuri. Ba wannan yan Nigeria ke son ji ba. Muna so ne a kawo karshen garkuwa da mutane," a cewar Baba-Ahmed cikin jawabinsa.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na'abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel