N234 ya kamata a rika sayar da litan mai, amma N162 ake sayarwa, Shugaban NNPC

N234 ya kamata a rika sayar da litan mai, amma N162 ake sayarwa, Shugaban NNPC

- Ministan Man Fetur ya bayyana cewa za'a kafa sabuwar doka kan man fetur a watan Afrilu

- Shugaban NNPC ya yi fashin baki kan lamarin tallafin man fetur

- Yan Najeriya sun lashi takobin zanga-zanga idan aka kara farashin man fetur

Shugaban kamfanin man feturin Najeria (NNPC), Mele Kyari, ya bayyana cewa kowani wata ana biyan kudin tallafin man fetur na kimanin bilyan 100 zuwa 120.

Kyari ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin hira da manema labarai a taron da kwamitin yada labaran fadar shugaban kas ata shirya, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ya tabbatar da cewa har yanzu gwamnatin Buhari na biyan kudin tallafn mai.

A watan Mayu na shekarar 2016, farashin litan mai ya tashi daga N80 zuwa N145.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa farashin ya tashi ne saboda ta daina bada tallafin man fetur.

Amma yanzu shugaban NNPC ya ce ba zai yiwu a cigaba da sayar da litan mai fetur N162 ba.

Ya yi jawabinsa bayan karamin Ministan arzikin mai, Timipre Sylva, ya bayyana lokacin da za'a samar da sabuwar dokar kamfanin man fetur (PIB).

KU DUBA: Wata bakuwar cuta ta bulla jihar Sokoto, ta kashe dalibi 1, ta kwantar da 30

N234 ya kamata a rika sayar da litan mai, amma N162 ake sayarwa, Shugaban NNPC
N234 ya kamata a rika sayar da litan mai, amma N162 ake sayarwa, Shugaban NNPC Credit: @NNPC
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalilin da ya sa muka ce wajibi ne a bar dalibai mata su sanya Hijabi a makarantu, gwamnan jihar Kwara

Kyari ya ce bayanan dake cikin takardunta sun nuna cewa N234 ya kamata a rika sayar da litan mai, amma N162 ake sayarwa.

Ya ce wajibi ne a bari tashi da saukan farashin danyan man su rika gudanar da yadda farashin litan tataccen mai zai kasance.

Ya kara da cewa kawai gwamnati ta yi tunanin irin halin da yan Najeriya zasu shiga ne idan aka wajabta musu sayan mai a farashin da ya kamata.

A bangare guda, kamfanin mai na kasa watau NNPC, ya ce babu karin farashin man fetur da za ayi a wannan watan na Maris.

NNPC ya gargadi mutane a kan sayen mai da ake ta yi a tsorace har ana boye wa, ya ce ba za a gamu da wani karin farashin lita a watan Maris, 2021 ba, Wannan bayani akasin rahotannin da su ke yawo ne na cewa farashin lita zai tashi.

Kamfanin yake cewa ba za su so su jefa ‘Yan Najeriya a wahala ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel