Shirin kara farashin fetur: Gwamnatin Buhari ba ta da tausayin talakawan Najeriya, TUC

Shirin kara farashin fetur: Gwamnatin Buhari ba ta da tausayin talakawan Najeriya, TUC

- Kungiyar TUC ta yi Alla-wadai da shirin kara farashin man fetur

- A cewar TUC, gwamnatin nan ta san abinda ya kamata amma ba zata yi ba

- Najeriya na da arzikin man fetur amma ba ta iya tace manta da kanta sai ta kai kasar waje

Kungiyar yan kwadago TUC ta caccaki gwamnatin tarayya kan sabon shirin da take yi na kara farashin man fetur sakamakon karuwan farashin danyen mai zuwa $60 ga ganga a kasuwan duniya.

TUC ta bayyana cewa gwamnatin nan ba ta tausayin yan Najeriya gaba daya, The Nation ta ruwaito

A jawabin da shugaban kungiyar, Kwanred Quadri Olaleye, ya saki, ya ce gwamnati na azarbabin fadawa Najeriya farashi zai tashi amma ba ta gaggawa wajen cika alkawuranta.

"Kungiyar TUC ta yi matukar girgiza kan maganan da aka ce ma'aikatar man fetur ta saki na karin da farashin danyen mai yayi a kasuwar duniya," Jawabin yace.

"Tambayar itace me yasa gwamnati ke gaggawan fada mana karin farashin danyen mai da kuma yiwuwan karuwar farashin fetur; amma sai ta kwashi makonni ko watanni kafin cika alkawarin da ta yiwa kungiyoyin kwadago?"

"Kawai wannan abu daya yake nuni: ba su tausayin talakawa a kasar nan."

"Najeriya na cikin kasashe shida mafi arzikin mai a duniya. Rahotanni sun nuna cewa namu na cikin mafi kyau, amma mun gaza cin gajiyar haka. Matatun man mu hudu basu aiki."

"Yanzu Najeriya na dogara kan Dangote da jamhuriyyar Nijar su bamu mai! Dangote mutum daya ne, yayinda Nijar ko Legas bata kai yawan jama'a ba."

KU DUBA: Cin hanci da rashawa na hau-hawa ne saboda ba a daure masu laifi, in ji Amaechi

Shirin kara farashin fetur: Gwamnatin Buhari ba ta da tausayin talakawan Najeriya, TUC
Shirin kara farashin fetur: Gwamnatin Buhari ba ta da tausayin talakawan Najeriya, TUC
Asali: Facebook

DUBA NAN: Zulum ko tawagarsa ba suyi hadarin mota ba, Mai magana da yawunsa yayi martani

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Cif Timipre Sylva ya gargadi ‘yan Nijeriya da su kasance cikin shirin jure wahalar karin farashin mai yayin da farashin danyen mai ya haura sama da $60 a kowace ganga.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin Inganta Kudin Najeriyar a ranar Talata, Sylva ya ce ba tare da samar da tallafi a cikin kasafin kudin 2021 ba, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC), ba zai iya ci gaba da daukar nauyin da ke kasa-kasa ba.

A halin yanzu, farashin man fetur ya kai N160 zuwa N165, farashin da aka sanya lokacin da danyen ya yi sama da $43 a kowace ganga, watanni hudu da suka gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng