Gwamnatin Tarayyar Nigeria na shirin yin ƙarin kuɗin dakon man fetur

Gwamnatin Tarayyar Nigeria na shirin yin ƙarin kuɗin dakon man fetur

- Gwamnatin tarayya na shirin kara farashin dakon man fetur daga N7.51 zuwa N9.11 duk lita

- Sakataren hukumar daidaita farashin man fetur, Ahmed Bobboi, ne ya bada sanarwar

- Gwamnatin ta ce tana tattaunawa da shugabannin kungiyoyin kwadago kuma idan ta kammala za ta bada cikaken bayani

Gwamnatin tarayyar Nigeria, FG, ta sanar da fara tattaunawa da wakilar kungiyoyin kwadago a kan yadda za a kara kudin dakon man fetur daga N7.51 zuwa N9.11 duk lita.

Wannan tsarin na nufin karin kashi 21.30 cikin dari a kudin dakon man fetur din.

Gwamnatin Tarayya na shirin kara kuɗin dakon man fetur
Gwamnatin Tarayya na shirin kara kuɗin dakon man fetur. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Gwamna Bala Mohammed: Yadda na kusa rasa aiki na saboda Jami'ar Baze

An bada wannan sanarwar ne bayan taron kungiyar masu motocin haya na kasa da ake yi a Zuma Rock Resort, a babban titin Abuja zuwa Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Sakataren hukumar daidaita farashin man fetur, Ahmed Bobboi, ya ce hukumar tana jiran amincewa daga gwamnatin tarayya kafin ta aiwatar da sabon farashin dakon na N9.11 duk lita.

Ya kuma ce FGn na fatan kungiyoyin ma'aikata za su amince da hakan kamar yadda aka cimma matsaya a gamayyar kwamitin da gwamnati ta kafa kan farashin man fetur da lantarki.

KU KARANTA: Kwamishina ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin gabatar da kasafin kudi a Enugu

Da aka bukaci ya yi tsokaci kan karin kudin dakon, shugaban hukumar NNPC, Mele Kyari, wanda ya samu wakilcin jami'in kudi na hukumar, Umar Ajiya, ya ce gwamnati za ta sanar da ranar karin bisa tsari.

Ya ce, "Sakataren PEF ya sanar cewa ana ganawa tsakanin FG da kungiyoyin kwadago kuma a karshe gwamnati za ta sanar da lokacin da za a fara amfani da farashin kamar yadda ya ke a tsarin farashi."

A wani labarain daban, babban malamin Kano, Shaikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce rufe masallacinsa da hana shi yin wa'azo da gwamnatin jihar ta yi "zalunci ne", kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da ke makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel