Dattawan Arewa sun ba Gwamnatin APC satar-amsa 3 domin magance matsalar tsaro

Dattawan Arewa sun ba Gwamnatin APC satar-amsa 3 domin magance matsalar tsaro

- Kungiyar Northern Elders’ Forum ta ce zaman lafiya ya gagara samuwa a Najeriya

- Hakeem Baba-Ahmed ya ce Buhari bai cika alkawuran da ya yi a 2015 da 2019 ba

- NEF ta ba gwamnatin tarayya shawarwari 3 na yadda za a samar da zaman lafiya

Darektan yada labarai da wayar da kai na kungiyar Northern Elders’ Forum, Hakeem Baba-Ahmed, ya soki gwamnatin APC mai-ci kan batun tsaro.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr Hakeem Baba-Ahmed ya na ikirarin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya gaza kawo zaman lafiya tun da ya hau mulki.

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin nan na Arise TV a ranar Laraba, 24 ga watan Maris, 2021.

KU KARANTA: Akwai alkawarin da aka yi na cewa barin Tinubu za su karbi mulki a 2023

Mai magana da yawun kungiyar dattawan na Arewa yake cewa shugaban kasa ya sa nawa wajen samar da zaman lafiya kamar yadda ya dauki alkawari.

Baba-Ahmed ya ce: “Idan na samu damar zama da shugaban kasa, zan fada masa: ‘Ran ka ya dade, ka farka, ka tsaya da kyau ka ji, kasar nan na neman kife wa.”

Ta na cikin babban hadari, Najeriya ta na fadi a karkashin idonka. Ka rantse a 2015 da kuma 2019 cewa za ka kare rayukan al’umma da ke cikin Najeriya.”

Ya ce: “’Yallabai, ka yi hakuri, ka gaza yin wannan, ko ba ka yi da kyau, ko ba ka yi gaba daya.”

Dattawan Arewa sun ba Gwamnatin APC satar-amsa 3 domin magance matsalar tsaro
Dr. Hakeem Baba Ahmed Hoto: Daily Trust
Source: UGC

KU KARANTA: Gwamnan Ebonyi ya caccaki PDP, Ibo sun fi morewa a mulkin APC

"Abin da ya kamata ka yi shi ne ka kiran mutanen Najeriya 200 zuwa 500, ba tare da wani sharadi ba, ka ce jama’a na yi imani za mu amfana da shawarwarinku.”

Sannan ya ce: “Na biyu, ka zauna da gwamnoninka. Su na da nauyi a kundin tsarin mulki, za su iya sauke wadannan nauye-nauye, musamman a harkar tsaro.”

Sai abu na uku, Baba-Ahmed ya ce Buhari ya tsaya ya tambaya domin jin inda aka samu matsala. “Ana yi kamar ba ayi, kullum mu na kara zama cikin rashin tsaro.”

A makon nan kun samu labari 'Yan bindigan da su ka yi awon gaba da da malaman makaranta a garin Birnin Gwari sun nemi a biya N15m a matsayin kudin fansa

A dalilin haka ne kungiyar CCNSE ta caccaki hafsoshin tsaro saboda sun zabi su yi aiki daga Abuja, CCNSE ta ba hasoshin shawarar su tare a Arewa maso gabas.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng News

Online view pixel