'Yan Kudu sun fi morar shekaru 5 da Buhari ya yi a kan shekara 16 da PDP ta yi inji Gwamnan Ebonyi

'Yan Kudu sun fi morar shekaru 5 da Buhari ya yi a kan shekara 16 da PDP ta yi inji Gwamnan Ebonyi

- David Umahi ya ce mutanen Kudu maso gabas sun fi morar gwamnatin PDP

- Gwamnan jihar Ebonyi ya jero ayyukan da Muhammadu Buhari ya yi masu

- Bayan ya koma APC, gwamnan ya ce Ibo sun amfana da mulkin da ake yi yau

Mai girma gwamnan jihar Ebonyi, Mista David Umahi ya fito ya yi wasu kalamai da za su iya fusata babbar jam’iyyar hamayya ta PDP da ya baro.

Gwamna David Umahi ya bayyana cewa mutanen kudu maso gabas sun fi morar gwamnatin Muhammadu Buhari a kan sauran gwamnatocin PDP.

Jaridar Vanguard ta ce David Umahi ya bayyana wannan ne ta bakin kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’ummar jihar Ebonyi, Orji Uchenna Orji.

KU KARANTA: Tinubu ya yi wa Katsinawa Allah-ya-kyauta, ya bada N50m

Barr. Orji Uchenna Orji ya ce mutanen Kudu maso gabas sun fi cin moriyar gwamnatin APC ta fuskar tattalin arziki da samun abubuwan more rayuwa.

A cewar gwamnatin Ebonyi, daga cikin romon da yankin ya samu a mulkin Muhammadu Buhari akwai:

1. Gyaran filin tashi da saukar jirgin sama na Naira biliyan 10

2. Aikin gadar Neja ta biyu.

3. Hanyar Enugu zuwa Fatakwal

da sauransu

'Yan Kudu sun fi morar shekaru 5 da Buhari ya yi a kan shekara 16 da PDP ta yi inji Gwamnan Ebonyi
Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnonin da za su iya neman takarar Sanata a 2023

Dave Umahi ya cigaba da cewa:

“Wadannan alamu ne da cewa gwamnatin nan ta taimaka wa mutanen Kudu maso gabas fiye da kowa.”

Dazu kun ji cewa PDP ba ta dandara da 2019 ba, ana kishin-kishin za a ba Atiku Abubakar da Peter Obi tutar jam’iyya da nufin karbe mulki daga hannun jam'iyyar APC.

Wata majiya ta ce akwai yiwuwar PDP ta sake ba Atiku/Peter Obi tikitin kujerar Shugaban kasa.

Wasu manyan jam’iyyar hamayyar su na da ra’ayin shugaba Muhammadu Buhari bai lashe zaben 2019, don haka ake ganin Atiku zai iya doke duk wanda APC ta tsaida.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel