2023: Magoya bayan Tinubu sun fito sun bayyana tsohuwar yarjejeniyar da aka yi a APC

2023: Magoya bayan Tinubu sun fito sun bayyana tsohuwar yarjejeniyar da aka yi a APC

- SWAGA ta ce ACN da CPC sun yarda bangaren ACN ne za a ba takara a 2023

- Kungiyar ta ce an yi wannan magana tun 2014, amma ba a rubuta a takarda ba

- South West Agenda ta na yi wa Jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu fafatuka ne

Kungiyar South West Agenda wanda aka fi sani da SWAGA ta yi magana game da siyasar 2023, ta bayyana yarjejeniyar da aka yi wajen kafa jam’iyyar APC.

South West Agenda ta ce akwai alkawari da aka yi ta fatar baki tsakanin tsofaffin jam’iyyun CPC da ACN cewa bangaren ACN za su gaji kujerar shugaban kasa.

Wannan kungiya da ke goyon-bayan takarar jigon APC a kudu maso yammacin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, ta ce an yi wannan alkawari ne a shekarar 2014.

KU KARANTA: Takarar Bola Tinubu a 2023 ta na kara shiga jihohin Yarbawa

Mataimakin shugaban kungiyar SWAGA na kasa, Sanata Adesoji Akanbi, ya bayyana haka a lokacin da jaridar The Nation ta yi hira da shi a ranar Laraba.

Adesoji Akanbi ya ce ko da ba a rubuta wannan yarjejeniyar ba, an tsaida maganar a lokacin da ake yunkurin kafa jam’iyyar APC wanda ta samu mulki a 2015.

Sanata Akanbi wanda ya wakilci kudancin jihar Oyo tsakanin 2015 da 2019 ya ce shugabannin APC na yankin kudu sun yarda da wannan magana a lokacin.

A lokacin da aka yi maganar, Muhammadu Buhari ne shugaban barin ‘yan CPC, yayin da Asiwaju Bola Tinubu ya ke shugaban bangaren tsohuwar jam’iyyar ACN.

2023: Magoya bayan Tinubu sun fito sun bayyana tsohuwar yarjejeniyar da aka yi a APC
Tsohon Gwamna Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Watakila PDP ta sake ba Atiku/Peter Obi tikitin kujerar Shugaban kasa

A cewar Sanata Akanbi: “Akwai yarjejeniya tsakanin CPC da ACN a game da yadda za a rika juya takarar kujerar shugaban kasa, ko da ba a rubuta baro-baro ba.”

Shugaban na SWAGA ya ce: “Tunanin shi ne hakan zai rike Najeriya a dunkule. Mun yi imani ACN ta bada gudumuwa sosai wajen kafa jam’iyyar APC mai mulki.”

“Don haka mu ke ganin a bar yankin kudu su fito da shugaban kasan gobe.” Inji kungiyar.

“Mu a SWAGA, Asiwaju Bola Tinubu ne a gabanmu. Shi ne ‘dan takarar da zai iya lashe zabe a kudu maso yamma, shi ne wanda za a iya tallata wa sauran yankuna.”

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng