Barnar tsuntsaye ta ja jirgin sama da zai je Legas saukar gaggawa a Kano

Barnar tsuntsaye ta ja jirgin sama da zai je Legas saukar gaggawa a Kano

- Jirgin Aero Contractors yayi saukar gaggawa bayan tashin da yayi zuwa Legas daga jihar Kano

- Matuƙin jirgin ya yanke wannan shawarar ne bayan ƙarar da aka dinga ji a injin jirgin na dama

- Daga bisani an gano cewa tsuntsaye ne suka yi ɓarnar da ta taba farfelar jirgin, lamarin da ya kawo barzazanar

Sama da fasinjoji 100 da za su je Legas suka sha dogon zama a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano a ranar Lahadi bayan jirgin sama na Aero Contractors ya yi saukar gaggawa bayan mintuna kadan da tashinsa.

Kamar yadda ɗaya daga cikin fasinjojin dake jirgin ya sanar, jirgin ya tashi ne da karfe 9:30 na safe bayan an fara jin wata ƙara daga injin ɗin dama na jirgin wanda kusan dukkan fasinjojin suka ji.

Ya ƙara da cewa, jim kadan matuƙin jirgin ya sanar dasu cewa zai koma inda ya taso saboda ƙarar da ake ji.

KU KARANTA: Kalluba Tsakanin Rawuna: Jerin Mata 5 da Suka Taba Shugabancin Kasa a Afrika

Barnar tsuntsaye ta ja jirgin sama da zai je Legas saukar gaggawa a Kano
Barnar tsuntsaye ta ja jirgin sama da zai je Legas saukar gaggawa a Kano. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta

The Nation ta ruwaito cewa, an gano cewa tsuntsaye ne suka yi ɓarna a farfelar injin ɗin wanda ta yuwu yayi ɓarna.

Fasinjojin sun sauka kuma jami'an sun sanar dasu cewa suna jiran shawara daga hedkwatarsu dake Legas cikin sa'a ɗaya.

Bayan kusan sa'o'i biyar kuma babu jami'in da aka gani, fasinjojin sun bar filin jirgin domin neman madafa.

Amma kuma daga bisani kamfanin jiragen saman ya kira fasinjojinsa inda wasu suka samu jirgin tashi zuwa Legas na karfe 11 na dare.

Wani matukin jirgin sama yace hukuncin matuƙin jirgin yayi kyau domin hakan yasa ba a samu hatsari ba.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin NCAA, Sam Adurogboye yace an kaiwa hukumar rahoto a ofishinsu dake Kano.

"Manajan yanki na Kano ya tabbatar da cewa tsuntsaye ne suka yi ɓarnar. Za a kai jirgin Legas kamar yadda doka ta buƙata."

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Online view pixel