'Yan bindiga sun sheke 'yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi

'Yan bindiga sun sheke 'yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi

- Miyagun 'yan bindiga sun halaka jami'an 'yan sandan uku tare da kwashe makamansu

- Lamarin ya faru ne bayan 'yan bindigan sun budewa 'yan sandan wuta a kan titi yayin da suke duba motoci

- 'Yan sandan da aka kashe an bayyana sunansu da: Austin Ugwu, Longinus Ugochukwu da Ama Ifeanyi

'Yan bindiga sun sheke 'yan sanda uku a sabon harin da suka kai karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

The Cable ta gano cewa 'yan sanda da aka kashe a safiyar Litinin suna kan titi ne yayin da suke duba motoci masu wucewa.

An gano cewa 'yan sandan sun kai harin sannan suka yi awon gaba da bindigogin jami'an tsaron.

'Yan sandan da aka kashe sun hada da: Austin Ugwu, Longinus Ugochukwu da Ama Ifeanyi.

KU KARANTA: Bayan kanwarta tayi wuff da tsohon saurayinta, Fatima Indimi ta magantu kan yafiya

'Yan bindiga sun sheke 'yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi
'Yan bindiga sun sheke 'yan sanda 3 a Abia, sun yi awon gaba da bindigogi. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu

Ude Chukwu, mataimakin gwamnan jihar, ya kushe wannan harin yayin da ya kai ziyara yankin bayan sa'o'i kadan da aukuwar lamarin.

Ya kara tabbatarwa da mazauna yankin cewa gwamnatin jihar za ta tura abubuwan da ake bukata.

Cigaban yazo ne kasa da wata daya bayan kashe wani jami'in dan sanda da aka yi a jihar bayan 'yan bindiga sun kutsa Aba.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da makamai daga ofishin 'yan sandan.

Lamarin da ya faru na nuna hauhawar rashin tsaro da kuma harin da ake kaiwa jami'an tsaro a yankin kudancin kasar nan.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya karba bakuncin Oladimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai da Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun a fadarsa dake Abuja.

Bankole da Daniel cikin kwanakin nan ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Yayin kai ziyarar fadar shugaban kasa, sun samu rakiyar Mai Mala Buni, Mohammed Badaru da Atiku Bagudu, gwamnonin Yobe, Jigawa da Kebbi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel