Ba za mu bada kunya ba, dukkan kallo ya dawo kanmu, Shugaban EFCC Bawa

Ba za mu bada kunya ba, dukkan kallo ya dawo kanmu, Shugaban EFCC Bawa

- Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, yace ba zasu gaza ba wurin sauke nauyin dake kansu

- Bawa ya sanar da jami'an hukumar cewa yanzu haka idon 'yan Najeriya da duniya baki daya yana kansu ne

- Ya hori jami'an hukumar da su kasance masu da'a tare da nuna kwarewarsu a cikin dukkan ayyukansu

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), yace hukumar ba za ta gaza ba wurin sauke nauyin al'umma dake kanta.

A yayin jawabi a ranar Litinin yayin da ya ziyarci ofishin hukumar dake jihar Sokoto, Bawa ya sanar da jami'an cewa yanzu dukkan kallo ya dawo kansu.

Kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa, ya bukaci jami'an da su kasance masu da'a da kuma yin ayyukansu cike da kwarewa.

KU KARANTA: Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai

Ba za mu bada kunya ba, dukkan idanu sun dawo kanmu, Shugaban EFCC Bawa
Ba za mu bada kunya ba, dukkan idanu sun dawo kanmu, Shugaban EFCC Bawa. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini

"Tuni mun yi alkawarin cewa zamu yi iyakar iyawarmu kuma ba za mu gaza ba. Idanun 'yan Najeriya da duniya baki daya ya dawo kanmu," Bawa yace.

Bawa ya kara da jan kunnensu inda yace "hukumar ba za ta lamunci kowanne irin aiki na rashin da'a ba kuma za ta magance hakan kamar yadda doka ta bukata."

Yayin jawabi kan matsalolin ma'aikata na cikin gida, yace "ganin cewa daga cikinku aka zabe ni, na san duk wasu matsalolin da ke kasa, daga karin girma, walwala da sauransu.

"Ina tabbatar muku da cewa tuni aka kafa kwamitoci da zasu duba lamurran kuma su kawo hanyar shawo kansu da tabbatar da hakan da gaggawa."

Tuni dai shugaban EFCC ya ziyarci ofisoshinsu na Abuja da Kaduna.

A wani labari na daban, sama da fasinjoji 100 da za su je Legas suka sha dogon zama a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano a ranar Lahadi bayan jirgin sama na Aero Contractors ya yi saukar gaggawa bayan mintuna kadan da tashinsa.

Kamar yadda ɗaya daga cikin fasinjojin dake jirgin ya sanar, jirgin ya tashi ne da karfe 9:30 na safe bayan an fara jin wata ƙara daga injin ɗin dama na jirgin wanda kusan dukkan fasinjojin suka ji.

Ya ƙara da cewa, jim kadan matuƙin jirgin ya sanar dasu cewa zai koma inda ya taso saboda ƙarar da ake ji.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Online view pixel