Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji

- Sojojin Najeriya za su yi maganin ‘Yan bindigan da su ka addabi kasar nan

- Dakarun sojoji za su shiga kungurman jeji su yiwa ‘Yan bindiga luguden wuta

- Gwamnonin Arewa maso yamma sun bada umarnin kowa ya fito daga daji

Shugaban hafun sojojin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ce dakarunsa sun kammala shirin ganin bayan ‘yan bindigan da ke kawo rashin zaman lafiya.

Da yake magana wajen taron da aka shirya a Abuja a kan sha’anin tsaro, Janar Lucky Irabor, ya ce za su bankado duk wadanda su ka fake a jeji su na ta’adi.

Daily Trust ta rahoto Lucky Irabor ya na cewa za a samu zaman lafiya nan ba da dadewa ba a kasar nan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi ta'adi a Kaduna, Ogun

Haka zalika mai girma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bada sanarwar cewa za a shiga jeji da duk wani kwararo domin a tsefe ‘yan bindiga.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin na Liberty TV.

Rt. Hon. Aminu Masari yake cewa: “Duk wanda ya rage a jeji, za mu dauke shi a matsayin ‘yan bindiga. Saboda haka, jami’an tsaro za su yi masu raga-raga.”

Aminu Bello Masari ya bayyana cewa gwamnonin yankin Arewa maso yamma za su yafe wa ‘yan bindigan da su ka tuba, su ka fito su ka ajiye kayan fadansu.

KU KARANTA: Ka gaza - Fayose ga Buhari

Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji
Shugaban hafun sojojin Najeriya, Janar Lucky Irabor @HQArmy
Source: Facebook

Ministan tsaro na kasa, Janar Salihi Magashi mai ritaya, ya ce sojoji za su shiga jeji su ga bayan ‘yan bindiga kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi umarni.

Da yake magana wajen taron da aka shirya na kwana daya, Magashi, ya ce ana cikin tsaka mai wuya a dalilin hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.

Dazu kun ji cewa Abdullahi Ganduje ya fito ya ce harin da aka kai wa Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohin kasar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya ce abokan aikinsa sun damu a dalilin harin da aka kai wa takwaransu, Samuel Ortom, duk da tsaron da yake da shi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel