Adebanjo: Wasan yaudara ake yi tsakanin Tinubu da Buhari, ba za a ba Tinubu mulki a 2023 ba

Adebanjo: Wasan yaudara ake yi tsakanin Tinubu da Buhari, ba za a ba Tinubu mulki a 2023 ba

- Idan Bola Tinubu ya nemi tikitin APC a zaben 2023, ba zai samu nasara ba

- Wannan shi ne ra’ayin sabon shugaban kungiyar Afenifere, Ayo Adebanjo

- Ayo Adebanjo ya ce Shugaba Buhari ba zai ba Bola Tinubu mulki a 2023 ba

Sabon shugaban kungiyar da ke kare hakki da muradun Yarbawa a kasar nan, Afenifere watau Cif Ayo Adebanjo, ya tabo batun siyasar 2023.

Ayo Adebanjo ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai mika ragamar kasar nan ga babban jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu ba.

Da aka yi hira da dattijon a jaridar Punch, ya bayyana cewa shugaban Najeriyar da tsohon gwamnan na jihar Legas su na yaudarar junansu ne.

KU KARANTA: Zan marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023 - Buhari

Adebanjo ya yi amfani da damar, ya yi kaca-kaca da Tinubu, Yemi Osinbajo da gwamnonin Kudu na shirin da su ka yi kan batun sauya fasalin kasa.

Cif Adebanjo yake cewa: “Wanda ya fita dabam shi ne gwamnan jihar Oyo, Makinde, sauran duk su na tare da Tinubu, shi kuma ya na tare da Buhari.”

“Amma duk yaudarar juna su ke yi, shugaban kasa Muhammadu (Buhari) ba zai mika masa (Bola Tinubu) mulki ba, don sun goyi bayansa (Buhari)”

“Na fada a fili kafin yanzu, kuma zan sake nanata wa, Buhari ya na yaudarar Tinubu ne, shi ma Tinubu ya na yaudarar Buhari ne.” inji Ayo Adebanjo.

KU KARANTA: Gwamnan Edo ya sake samun galaba a kotu, ya doke Jam’iyyar APC

Adebanjo: Wasan yaudara ake yi tsakanin Tinubu da Buhari, ba za a ba Tinubu mulki a 2023 ba
Chief Ayo Adebanjo Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

“Ni tsoho ne, mai jiran mutuwa a halin yanzu, saboda haka ka je ka ce ni na fada; Idan Tinubu ya shiga zaben fitar da gwani a APC, ba zai yi nasara ba.”

Shugaban na Afenifere ya ce Buhari zai so ya mika mulki ne ga Fulani, ya yi kira ga Tinubu da gwamnoni su sake tunani, su dawo tafiyar kungiyar.

A shekarar bara kun ji cewa wata kungiyar siyasa da ta ke neman jigon APC, Bola Tinubu, ya fito takarar shugaban Najeriya a zaben 2023, ta bayyana.

Wannan kungiyar da ta fito mai suna Tinubu 2023, Not Negotiable wanda aka fi sani da TNN, ta ce ta samu mutane miliyan daya da ke goyon-bayan Tinubu.

An dade ana hurowa tsohon gwamnan ya nemi takara domin ya gaji shugaba Muhammadu Buhari.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel