Digirin bogi: Gwamnan Edo ya tsallake tarkon APC, ya samu nasara a shari’ar da ake ta yi

Digirin bogi: Gwamnan Edo ya tsallake tarkon APC, ya samu nasara a shari’ar da ake ta yi

- Alkali ya zartar da hukunci a shari’ar Godwin Obaseki da jam’iyyar APC

- APC ta na ikirarin Gwamna Obaseki ya na amfani da shaidar Digirin bogi

- An yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar, Alkali ya kuma ci ta tara

A ranar Alhamis, 18 ga watan Maris, 2021, babban kotun daukaka kara da ke zama a Abuja, ya yi watsi da karar da APC ta kai gwamna Godwin Obaseki.

Jam’iyyar APC ta na zargin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da amfani da takardun bogi. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Alhamis.

Alkalin babban kotun tarayyar ya yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar, ya ce ba ta da wasu hujjojin na a zo a gani, ya bukaci a ba gwamnan N250, 000.

APC ta ce gwamnan na jihar Edo ya na amfani ne da satifiket din digiri na jami’ar Ibadan na bogi. Alkali ya ce zargin da lauyoyin APC su ke yi kanzon kerege ne.

KU KARANTA: Ihu bayan hari: Bala Mohammed ya ce PDP ta doke Buhari a 2019

Stephen Adah ya saurari shari’ar da aka daukaka, ya zartar da hukunci a ranar Alhamis, inda ya tabbatar da hukuncin farko da ya ba Godwin Obaseki gaskiya.

Mai shari’a Stephen Adah ya dogara ne da hujjar da wani babban jami’in jami’ar tarayyar Ibadan, Abayomi Ajayi, ya bada a game da shaidar samun digirin Obaseki.

Abayomi Ajayi ya tabbatar wa kotu cewa Obaseki ya halarci jami’ar Ibadan a 1976, kuma ya kammala.

Babban kotun daukaka karan ta ce hujjojin da Ajayi ya gabatar sun gamsar da Alkali cewa babu shakka wanda ake zargin ya na dauke ne da satifiket na ainihi.

Digirin bogi: Gwamnan Edo ya tsallake tarkon APC, ya samu nasara a shari’ar da ake ta yi da shi
Gwamnan Edo, Godwin Obaseki Hoto: www.godwinobaseki.com
Source: Twitter

KU KARANTA: An hurowa Hadimin Buhari wuta ya yi murabus kan zargin 'kudin makamai’

Adah ya ce lauyoyin da su tsaya wa jam’iyyar APC mai adawa a jihar Edo ba su iya kare zarginsu na cewa gwamna Obaseki ya na amfani da takardun karya ba.

Kafin yanzu, wani Alkalin babban kotun tarayya a Abuja, Ahmed Ramat Mohammed, ya saurari wannan kara, ya kuma yi fatali da ita a watan Junairu, 2021.

Alkali mai shari’an yake cewa tamkar wani daga waje ne ya shiga har cikin gidan mutum, ya na fada masa cewa ba shi ne mahaifin duk ‘ya ‘yan da ya haifa ba.

Wani jigon APC, Williams Edobor ne ya shigar da wannan kara a madadin jam'iyyar ta APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit

Online view pixel