Zan marawa Bola Tinubu baya a 2023 - Buhari

Zan marawa Bola Tinubu baya a 2023 - Buhari

- Babban jigon APC, Bola Tinubu, ya fara samun magoya baya tun yanzu kan lamarin takaran 2023

- Jam'iyyar APC a jihar Ekiti na fama da rikicin cikin gida, kuma lamarin takarar shugaban kasa na ciki

- Tun yanzi an fara sharan faggen yakin neman shugabancin kasa a 2023

Jita-jitan da ke yaduwa na niyyar takkarar shugaban kasan tsohon gwamnan jihar Legas kuma babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya fara zama gaskiya.

Manyan yan siyasa a yankin kudu maso yamma inda jihohin kabilar Yarbawa suke sun lashi takobin goyawa Tinubu baya ya gaji shugaba Buhari.

Wani Sanata mai wakiltan Oyo ta Arewa, AbdulFatai Buhari, ya bayyana cewa lallai zai goyawa Tinubu baya ya zama shugaban kasan Najeriya a 2023 idan ya yanke shawarar takara.

Buhari ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da dan jaridar Edmund Obilo, a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2020.

Yayinda aka tambayeshi shin da gaske ne gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, na yaki da hadafin Bola Tinubu, Buhari ya ce ba gaskiya bane.

"A'a. Na mabiyin Tinubu ne. Ni ba na Fayemi bane kuma ba zan shiga cikin wadanda ke kokarin yaki da Tinubu ba. Ni magoyi bayan Tinubu ne, " Yace

DUBA NAN: Adadin mutanen da yan Boko Haram suka kashe a harin da su kaiwa gwamna Zulum

Zan marawa Bola Tinubu baya a 2023 - Buhari
Zan marawa Bola Tinubu baya a 2023 - Buhari
Source: UGC

KARANTA: Zulum ya cika alkawari, ya baiwa iyalan kwamandan Sojan da aka kashe N20m

A wani labarin daban, Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyoyin sufurin jiragen sama guda hudu, za su bi sahun kungiyar kwadago ta kasa NLC, shiga yajin aiki a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, kungiyoyin sun bukaci ma'aikatansu a sufurin jiragen sama da su yi zamansu a gida daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel