Rikicin Hijabi: Karka Jefa Najeria Cikin Yaƙi Kan Hijabi, Shugaban PFN ya Gargaɗi Gwamnan Kwara

Rikicin Hijabi: Karka Jefa Najeria Cikin Yaƙi Kan Hijabi, Shugaban PFN ya Gargaɗi Gwamnan Kwara

- Wani shugaban kiristoci ya yi kira ga gwamnan kwara kan ya bi lamarin hijabin nan a sannu don gudun jawo babban matsala a ƙasar nan.

- A cewar sa wannan lamarin na da sarƙaƙiya kuma idan ba'a ɗauki matakin da ya dace ba zai iya jawo yaƙi a ƙasar nan.

- Ya kuma taɓo maganar ƙarin wa'adi da shugaban ƙasa ya yi wa shugaban rundunar 'yan sandan ƙasar nan Muhammad Adamu

Shugaban wata ƙungiyar mabiya addinin kirista ta PFN, Bishof Wale Oke, ya gargaɗi gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdul-rahman Abdulrasaq.

Shugaban ya yi gargaɗin ne kan kada gwamnan ya kuskura yafara wani abu da zai iya kai ƙasar nan ga yaƙi.

Ya ce rikicin hijabi dake faruwa a jihar ka iya zama sababin hakan matuƙar ba'a ɗauki matakin da ya dace ba.

KARANTA ANAN: Yaron Hadimar Uwargidar Buhari ya saye dirkekeiyar mota mai kamar za ta yi magana

Shugaban ya kuma taɓo maganar ƙarin wa'adi da aka yi ma shugaban rundunar 'yan sandan ƙasar nan, IGP Muhammad Adamu.

A cewarsa kamata ya yi iGP ya rubuta takardar aje aikinsa saboda gazawarsa a matsayin.

Oke, ya yi wannan jawabi ne a Ibadan ranar Litinin, ya yin da ya karɓi bakuncin mabiyansa daga jihohin Ekiti da Ondo, kamar yadda Punch ta ruwaito.

"Ina kira ga mai girma gwamna da ya daina shiga abun da zai jawo rikici a jihar, ka girmama al'ada da kuma imanin wasu. Ka guji saka siyasa a wasu lamurran don hakan ka iya saka ƙasar nan cikin yaƙi. Ka jawo kowa a jikinka, kada ka tilasta hijab kan mutanen mu, ba zasu amince su maka biyayya ba," inji Oke.

Rikicin Hijabi: Karka Jefa Najeria Cikin Yaƙi Kan Hijabi, Shugaban PFN ya Gargaɗi Gwamnan Kwara
Rikicin Hijabi: Karka Jefa Najeria Cikin Yaƙi Kan Hijabi, Shugaban PFN ya Gargaɗi Gwamnan Kwara Hoto: @FollowKWSG
Asali: Twitter

Rikici dai ya ɓarke a jihar tsakanin musulmai da kiristoci a kan abar ɗalibai mata musulmai su saka hijabi a wasu makaranru 10 a jihar ta Kwara.

Matsalar dai ta tilasta ma Gwamnatin jihar bada umarnin kulle makarantun a watan Fabrairun da ya gabata.

KARANTA ANAN: Bashir Dandago: Hukumar Tace Fina-Finai a Kano Ta Kama Mai Waƙoƙin Yabon Annabi

Sai dai a ranar Litinin ɗinnan aka koma aiki gadan-gadan a waɗannan makarantu, Ɗalibai da malaman makarantun sun koma makaranta cikin ɗar-ɗar musamman a makarantar Sakandiren Baftis dake Surelore, inda nan ne rikicin yafi ƙamari tsakanin muslmai da kiristoci.

Su dai Musulmai na kara jaddada dole abar yaran su su saka hijab kuma su shiga makarantun kamar yadda kotu ta bada umarni, amma kiristoci na cewa hakan ba mai yuwu wa bane.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun kashe shugaban wasu Fulani a jihar Kaduna

Lawal Musa, shugaban al'ummar Fulani a karamar hukumar Kajuru da ke Kaduna, ya rasa ransa sakamakon wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwarsa, ta kuma yi Allah wadai da lamarin.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: