Ga su can a daji: Ortom ya bukaci Buhari yayi maganin ƴan ta'addan Binuwai
- Dr Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai ya buƙaci shugaban Buhari da ya tsamo ƴan ta'addan dake addabar jiharsa
- A cewar gwamnan yayi gudun famfalaki na tsawon kilomita daya da rabi yayin da ƴan bindiga suka kai masa hari
- Ortom ya bayyana cewa matukar ba zai iya zuwa gona ba, babu wanda zai iya zuwa a jihar, lamari mai bada tsoro
Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom a ranar Asabar yayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jami'an tsaro da su tsamo ƴan ta'addan da suka addabi jiharsa.
Ortom yayi magana da manema labarai bayan tsallake harin da ake zargin makiyaya ne suka kai masa a garin Makurdi.
Channels Tv ta ruwaito cewa, ya je kai ziyara wata gona yayin da maharan suka far masa amma jami'an tsaro dake tare da shi sun yi nasarar fatattakarsu.
KU KARANTA: Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai
KU KARANTA: Bidiyon Amarya mai Adon Fuka-fukai ya Janyo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta
Ortom yace yayi gudu na "sama da kilomita ɗaya da rabi ba tare da tsayawa ba" domin gujewa miyagun.
Binuwai tana ɗaya daga cikin jihohin da rikicin manoma da makiyaya ya ƙi ci balle cinyewa.
"Ina godiya ga jami'an tsaron da ke tare da ni. Sun yi nasarar fatattakar maharan kuma basu ci galaba ba. Ina godiya ga Ubangiji da ya bani lafiyar da nayi gudun sama da kilomita ɗaya da rabi ba tare da tsayawa ba.
"Bani da wata matsala da Fulani amma ina da matsala da Fulani ƴan bindiga wadanda suka sha alwashin kai ƙasar Najeriya ƙasa.
"Nace a'a ba zai yuwu ba a lokacin da nake gwamnan jihata. Idan ba zan iya zuwa gona ba, waye kuma zai iya zuwa a jihar nan. Ku fahimci halin da Benue take ciki.
"Ina godiya ga shugaban ƙasa da yayi martani ga wasiƙata inda yace duk wanda aka kama da AK-47 a harbe shi a take. Har yanzu ban gani ba. Ina son ganin hakan a jihar Binuwai
"Na kaiwa jami'an tsaro rahoto kuma ina fatan za mu samu sassauci da zaman lafiya har mu koma gonakinmu mu samu abinci.
"Ina son yin kira ga shugaban kasa a kan cewa jami'an tsaro su tsamo waɗannan mutane. Suna dajin tsakin Makurdi da Abinse. Suna rayuwa a can kuma suna fitowa yin ɓarna."
A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.
Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng