Kalluba Tsakanin Rawuna: Jerin Mata 5 da Suka Taba Shugabancin Kasa a Afrika

Kalluba Tsakanin Rawuna: Jerin Mata 5 da Suka Taba Shugabancin Kasa a Afrika

- Mutuwar shugaba John Magufuli ta sa mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan na shirin karbar mulkin kasar

- Ba wannan bane karon farko da aka fara samun mace ta shugabancin kasa ba a Afrika, duk da za a ce a 2005 aka fara

- An samu mata shugabannin kasashe a Liberia, Malawi, Ethiopia, Mauritania da jamhuriyar Afrika ta tsakiya

A yayin da mataimakiyar shugaban kasar Tanzania, Samia Suluhu Hassan ke shirin karbar ragamar mulkin kasar bayan mutuwar shugaba John Magufuli, ga kalluba tsakanin rawuna a nahiyar Afrika da suka taba shugabancin kasa.

Liberia: Ellen Johnson Sirleaf

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kafa tarihi lokacin da ta zama shugaban kasa ta farko mace da aka zaba a 2005.

Masaniya a fannin tattalin arziki, tsohuwar ma'aikaciyar gwamnatin kuma ministan kudi ta samu zarcewa a karo na biyu a 2011.

Sirleaf ta yi kokarin wanzar da zaman lafiya a lokacin da kasar ke cike da tarzoma. Sai dai bata samu nasara a habaka tattalin arziki ba kuma talauci ya tsananta.

KU KARANTA: Gwamna Masari ya kalubalanci yadda Gumi yake wa 'yan bindiga, yana tafka kuskure

Kalluba tsakanin rawuna: Jerin mata 5 da suka taba shugabancin kasa a duniya
Kalluba tsakanin rawuna: Jerin mata 5 da suka taba shugabancin kasa a duniya. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sheke sojojin Najeriya 3 a jihar Zamfara

Malawi: Joyce Banda

Joyce Banda ta zama shugaban kasar Malawi a 2012 inda ta tashi daga matsayin mataimakiyar shugaban kasa bayan mutuwar shugaba Bingu wa Mutharika.

Ta bar kasar a 2014 bayan ta sha mugun kaye a zaben shugaban kasa kuma tana fuskantar tuhuma akan wata harkallar kudade da ake yi.

Central African Republic: Samba Panza

Lauya Catherine Samba Panza an zabeta a 2014 a matsayin shugaban kasa ta mika mulki daga sojoji zuwa farar hula bayan kasar ta cika da yaki.

Ta rike wannan matsayi har 2016 kuma ta nemi shugabancin kasa a 2020 amma an maka ta da kasa.

Mauritania: Ameenah Gurib-Fakim

Ameenah Gurib-Fakim ta samu shiga majalisar dattawa a 2015 inda ta zama ta farko macen da ta taba rike wannan matsayin.

Bayan kama ta da aka yi da almundahanar wasu kudade, ta yi murabus a 2018.

Ethiopia: Sahle-Work Zewde

Sahle-Work Zewde an zabeta a matsayin shugaban kasa a 2018 a majalisar kasar, lamarin da yasa ta zama mace ta farko da ta taba rike wannan mukamin a kasar.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta damke wani matashi da yayi sanadin mutuwar wani dattijo mai shekaru 60 kuma mahaifin abokinsa bayan ya lakada masa mugun duka.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin a yammacin Talata.

Lamarin ya faru ne a unguwar sheka dake birnin Kano sakamakon takaddamar da ta hada matashin da mahaifin abokinsa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel