Muna cikin hali mai wuya, makiyaya 30 da shanu 322 sun bace a Anambra: Kungiyar Miyetti Allah
- Kungiyar MACBAN ta shigar da kara hedkwatar hukumar yan sandan Najeriya
- A cewar shugaban kungiyar, an kashe makiyaya a jihar Anambara
- Kungiyar ta bayyyana wasu kananan hukumomi hudu da wadannan abubuwan ke faruwa
Kungiyar Makiyayan Shanu a Najeriya, Miyetti Allah (MACBAN) ta kai kuka wajen hukumar yan sanda kan yawan kisan da ake yiwa Fulani a jihar Anambara.
Kungiyar MACBAN ta ce hare-haren da ake kai wa Fulani Makiyaya a jihar Anambara ya fara wuce gona da iri.
Vanguard ta rahoto cewa Miyetti Allah ta ambaci wasu kananan hukumomi hudu da wadannan hare-hare suka fi aukuwa.
Sun hada da karamar hukumar Ayamelum, Anambra ta gabas, Orumba South, da dunukofia.
Shugabannin Miyetti Allah sun kai kukansu ofishin mataimakin Sifeto Janar na yan sanda a Abuja.
A wasikar shugaban yankin kudu maso yamma, Gidado Siddiki, ya rattafa hannu, ya ce an yi rashin rayuka a wadannan hare-hare.
Ya kara da cewa yanzu haka Fulani makiyaya 30 sun bace kuma an nemi shanu 322 an rasa.
"Rayukan mambobin MACBAN na cikin hadari a wuraren an. Saboda haka muna kira taimako daga gareku domin dakile asarar rayuka da dukiya," wani sashen jawbain yace.
KU KARANTA: Gandollar: Sai mun kunyata wadanda suka kulla min sharri, Ganduje
DUBA NAN: Za a yiwa malaman addini alluran rigakafin Korona saboda su jawo hankalin mabiyansu
A wani kuwa, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya nuna goyon bayansa a kan amfani da karfi da kuma tattaunawa da 'yan fashin daji da ke kisa da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Ganduje ya jaddada cewa zama a tattauna da tubabbun 'yan fashi na da muhimmanci musamman ga mutanen da aka yi garkuwa 'yan uwansu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, a ranar Juma’a, 19 ga watan Maris.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng