Da duminsa: 'Yan bindiga sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Imo

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Imo

- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun bankawa ofishin 'yan sanda a jihar Imo wuta ya kone

- Kamar yadda aka tattaro, 'yan bindiga sun ci galaba a kan 'yan sandan inda suka saki wasu masu laifi

- 'Yan bindiga da tsageru na cigaba da cin karensu babu babbaka a yankin kudanci inda suke kaiwa jami'an tsaro hari

An babbake wata ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo.

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan bindiga ne suka rinjayi jami'an 'yan sanda dake ofishin kuma suka saki wasu wadanda ke tsare ana zarginsu da laifuka.

Wannan yana daga cikin miyagun harin da ake kaiwa 'yan sanda dake yankin kudancin kasar nan.

'Yan bindiga na cigaba da kaiwa jami'an tsaro hari tun a makonni biyu da suka gabata.

KU KARANTA: Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Imo
Da duminsa: 'Yan bindiga sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Imo
Asali: Original

KU KARANTA: Monguno: Babu Hadin Kan da ya Dace a Tsakanin Hukumomin Tsaron Kasar nan

A ranar Juma'a, rundunar 'yan sandan jihar Anambra sun bankado wani hari da aka kaiwa ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Aguata ta jihar a ranar.

Amma bayan sa'o'i kadan, an kaiwa motar da ta kwaso wadanda ake zargi zata kaisu kotu a Ekwulobia, inda aka harbe jami'in gidan yari daya tare da sakin wadanda ake zargin.

Sa'o'i ashirin da hudu kafin aukuwar lamarin, an halaka 'yan sanda da sojan ruwa a wurare mabanbanta a fadin jihar.

Wani mutum dauke da bindiga ya sakarwa 'yan sanda uku ruwan wuta a Neni dake karamar hukumar Anaocha ta jihar yayin da ya bankawa motarsu wuta.

A wani labarai na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.

Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel