Hoton matashin bature sanye da kayan NYSC ya janyo cece-kuce

Hoton matashin bature sanye da kayan NYSC ya janyo cece-kuce

- Wani farin matashin yayi suna a kafar sada zumuntar zamani na Twitter bayan ya wallafa hotunan kansa a cikin kayan NYSC

- Saboda launin kalar fatarsa da kuma yanayin gashin kansa, jama'a da dama sun dinga mamakin irin kaunar da yake wa Najeriya

- Mutane sun dinga shawartarsa da yayi amfani da launin fatarsa wurin cimma bukatunsa a sansanin NYSC

Wani matashi mai amfani da sunan @Linovin_ wanda yayi kama da dan nahiyar Asia amma yana yin hidimar kasa kuma hotunansa sun janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

A yayin da ya wallafa hotonsa sanye da kayan hidimar kasa, @Linovin ya rubuta "Dan Najeriya. Koyaushe kuma har abada."

Jama'a da dama sun yi martani da tambayoyi masu yawa a kan tsatson matashin. Yayin da wasu suke zargin ruwa biyu ne, wasu na zargin an haifeshi ne kawai a Najeriya.

KU KARANTA: Kalluba Tsakanin Rawuna: Jerin Mata 5 da Suka Taba Shugabancin Kasa a Afrika

Hoton matashin bature sanye da kayan NYSC ya janyo cece-kuce
Hoton matashin bature sanye da kayan NYSC ya janyo cece-kuce. Hoto daga @Linovin
Source: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram Sun Tsinke Wutar Lantarkin Maiduguri, Mazauna Suna Fama da Kudin Fetur

Amma kuma, a yayin rubuta wannan rahoton, Legit.ng bata tabbatar da duk wadannan hasashen ba.

Idan aka duba shafin matashin, za a gane cewa ya dade a Najeriya kuma ya san duka kananan kalmomin da gayu ke amfani dasu. Ya rubuta "cheee" a wallafofiinsa da dama.

Wallafarsa ta janyo dukkan tsokaci. Ga wasu daga ciki:

@me_gracie_ ta tambaya: "Tsawon wanne lokaci ka dauka a Najeriya? Tambaya ce kawai."

@skaddybaracuda cewa tayi: "Kana shakatawa gaye! Manta da surutun ka ji dadin shekarar hidimar kasarka dan uwa. Ina taya ka murna."

A wani labari na daban, wata mai raino, Anthonia Uchenna, wacce ta taba aiki a gidan tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ta ce tsohon ministan ya taba umartar masu tsaron lafiyarsa da su yi mata tsirara kuma suka zaneta.

Uchenna, wacce ta ziyarci ofishin Punch, ta sanar da rayuwarta dalla-dalla a gidan.

Ta ce tsohon ministan yayi amfani da 'yan sanda sau babu adadi wurin tsareta.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel