Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Arziki a Nigeria a Shekarar 2021

Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Arziki a Nigeria a Shekarar 2021

Nigeria na daya daga cikin manyan kasashe a nahiyar Afirka kuma tana da mutane fiye da miliyan 200.

Akwai jihohi 36 a kasar da babban birnin tarayya Abuja.

Domin gano jihar da ta fi arziki a Nigeria, yana da muhimmanci a duba alkalluman karfin tattalin arzikin cikin gida wanda ya kunshi dukkan cinikayya na jihar wato GDP.

Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Arziki a Nigeria a Shekarar 2021
Jerin Jihohi 10 da Suka Fi Arziki a Nigeria a Shekarar 2021. Hoto: @nairaland
Source: Twitter

Ga jerin jihohi 10 da suka fi arziki a Nigeria kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

1. Lagos - $33.68 biliyan

Legas ce kan gaba cikin jerin jihohin da suka fi arziki a Nigeria. Ita ce jihar da ta fi saura cigaba. Jihar na da fadin kasa na sakwaya kilomita 3,577 da GDP na $33.68 biliyan.

2. Rivers - $21.17 biliyan

Rivers na daya daga cikin jihohi masu arziki a Nigeria. Tana da fadin kasa na Sakwaya kilomita 11,077. Yawan jama'ar jihar ya kai miliyan 5.2 sannan GDP dinta $21.17 biliyan. Jihar ce kan gaba wurin albarkatun man fetur da gas.

DUBA WANNAN: Raba Gardama: Gwamnatin Kwara Ta Ce Dalibai Musulmi Na Iya Saka Hijabi a Dukkan Makarantunta

3. Delta - $16.75 biliyan

Jihar Delta na yankin kudancin Nigeria, tana da yawan mutane da suka kai miliyan 4.1. GDP na jihar ya kai $16.75 biliyan. Jihar na da man fetur da gas da albarkatun kasa kama kaolin, lignite, silica sa sauransu.

4. Oyo - $16.75 biliyan

Jihar Oyo na yankin Kudu maso Yammacin Nigeria. Adadin mutanen jihar ya kai miliyan shida. GDP na jihar $16.12 biliyan. Jihar na noman kayayyaki kamar shinkafa, doya, masara, cocoa, man ja, gero da sauransu.

5. Imo - $14.21 biliyan

Imo jiha ce da ke yankin Kudu maso Gabashin Nigeria. GDP na jihar $14.21 biliyan. Imo na da albarkatu da suka hada da man fetur, iskar gas, zinc, lead da sauransu. Manyan kamfanonin man fetur a jihar sun hada a Agip, Royal Dutch Shell, Chevron Corporation.

6. Kano - $12.39 biliyan

Yawan mutane da ke jihar Kano sun kai kimanin miliyan 11 sannan GDP na jihar ya kai $12.39 biliyan. Kano ta yi fice wurin samar da fatar dabobi domin sarrafa abubuwa da dama da noman auduga, wanken soya, ridi, tafarnuwa da sauransu.

7. Edo - $11.89 biliyan

Benin City ne babban birnin jihar Edo. Yawan mutanen jihar ya kai miliyan 3.5 da GDP na $11.89 biliyan.

8. Akwa Ibom - $11 biliyan

Akwa Ibom jiha ce da ke Kudancin Nigeria.Tana da yawan mutane da suka kai miliyan 5.5. Kabilun da suka fi yawa a jihar sun hada da Ibibio, Annang, Oron, Eket da Obolo. GDP din ta ya kai $11 biliyan.

KU KARANTA: Hijabi: Idan Rikici Ya Barke, Gwamnan Kwara Za a Tuhuma, Kungiyar CAN

9. Ogun - $11 biliyan

Ogun na yankin kudu maso yammacin Nigeria. Yawan mutanen jihar ya kai miliyan hudu. Akwai manyan kamfanoni da yawa a jihar kamar kamfanin simintin Dangote, kamfanin simintin Lafarage da sauransu. GDP na jihar $11 biliyan.

10. Kaduna - $10.33 biliyan

Kaduna jiha ce da ke yankin Arewa maso Yamma. Yawan mutanen jihar sun kai miliyan 6.1. Akwai kabilu da dama a jihar. GDP na jihar ya kai $10.33 biliyan.

A wani rahoton daban, kun ji cewa Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magafuli ya rasu sakamakon ciwon zuciya kamar yadda mataimakiyarsa Samia Suluhu Hassan ta sanar.

Suluhu Hassan yayin jawabin da ta yi wa yan kasar kai tsaya ta kafafen watsa labarai, ta sanar da rasuwarsa inda ta ce za a yi zaman makoki na kwanaki 14 a kasar.

A cewar mataimakiyar shugaban kasar, Mr Magafuli ya rasu ne a yammacin ranar Laraba 17 ga watan Maris na shekarar 2021 a asibiti a Dar es Salaam.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit

Tags:
Online view pixel