Gwamnatin Najeriya ta samu tallafin biliyan N338 don habbaka kiwon lafiya

Gwamnatin Najeriya ta samu tallafin biliyan N338 don habbaka kiwon lafiya

- Gidauniyar Global Fund ta ba gwamnatin Najeriya tallafin kudi har biliyan N338

- Kungiyar wacce ta saba bayar da tallafi ga kasashen duniya domin yaki da cutuka, ta ba Najeriya kudin domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ƙasar

- Hukumomin kasar ne suka bayar da sanarwar hakan a ranar Alhamis, 18 ga watan Maris

Gidauniyar Global Fund da ke bayar da tallafi don yaki da cutuka a kasashen duniya ta bai wa Najeriya tallafin kudi dala miliyan 890 (naira biliyan 338) domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ƙasar.

Idan za a tuna, a baya dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Najeriya da gidauniyar, har ta kai sai da ta yanke bai wa kasar tallafi.

A ranar Alhamis, 18 ga watan Maris ne hukumomin Najeriya suka bayar da sanarwar sabon tallafin.

Gwamnatin Najeriya ta samu tallafin biliyan N338 don habbaka kiwon lafiya
Gwamnatin Najeriya ta samu tallafin biliyan N338 don habbaka kiwon lafiya Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda ta halaka 'yan fashi 2 a wani artabu da suka yi a Jihar Kaduna

A tattaunawarsa da sashin Hausa na BBC, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya ce za a yi amfani da kudin wajen kula da cutuka irinsu tarin fuka da kanjamau da korona.

Ya ce:

“Kungiyar Global Fund abokiyar tafiya ce ga gwamnatin Najeriya kuma tare da hadin kan gwamnatin Amurka, ka ga dai irin wannan kudi masu dimbin yawa da suka ajiye da ake fata za a kashe su a Najeriya nan da shekara uku masu zuwa.

“Duk da haka, ka san tallafe ni ne in tallafa maka, mu kanmu Najeriya shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da muhimmin gudunmawa ta dala miliyan 12 a cikin wannan asusu, kuma kari ne a kan irin gudunmawa da ake bayarwa.

“Sannan muhimmin abunda nake so a fahimta shugaba Buari gyara ya kawo a kan dangantaka tsakanin Najeriya da Global Fund tunda a chan baya an aiko da kudi kuma an cinye su a Najeriya kuma suka ce sun yanke dangantaka da kowace hulda na yin irin wadannan aikace-aikace da gwamnatin Najeriya.

“Kuma shugaba Buhari ya sa aka yi hukunci mai tsanani aka kori wadancan jami’ai.

“Shi kamar bangaren masu kanjamau su kan ba da magunguna ga wajen mutum miliyan 1.2 a kowace shekara, sannan suna bayar da magani na malariya wajen miliyan 46.5 na yan Najeriya da kuma gidan sauro da suke bayarwa kusan miliyan 46.

“Sannan ciwon fuka wato TB su kan yi magani na wajen mutum dubu dari daya su kan warkar da su a shekara daya. Baya ga haka, suna bad a tallafi wajen yaki da cutar korona da yake sabo ne.

KU KARANTA KUMA: Yawan yaran da basa zuwa makaranta ya karu da miliyan 3 cikin watanni uku

“Don tuni suka bayar da gudunmawa mai tsoka ga gwamnatin Najeriya da aka fara siyo kayayyaki na kariya na jami’an lafiya da suke sawa wajen shiga asibiti da wajen marasa lafiya.”

A wani labari na daban, ministan ma'adinai da karafuna, Olamilekan Adegbite, ya cewa gwamnatin tarayya ta gano dimbin arzikin gwal a hanyar Abuja zuwa Nasarawa.

Ministan ya bayyana hakan yayinda ya kaiwa gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ziyara ranar Talata.

Adegbite yace an gano arzikin gwal din ne lokacin wani aikin hakan ma'adinai a hanyar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng