Atiku, Kwankwaso za su iya kai labari, PDP ta fadi yadda za ta fitar da ‘Dan takarar 2023

Atiku, Kwankwaso za su iya kai labari, PDP ta fadi yadda za ta fitar da ‘Dan takarar 2023

- Jam’iyyar PDP ta ce cancantar ‘dan takara za ta yi aiki a zaben 2023 ba yankinsa ba

- Kwamitin Bala Mohammed ya bayyana haka a rahoton aikin da yayi kan zaben 2019

- Idan aka tafi a haka, ‘Dan siyasar Arewa zai iya samun tikitin takarar shugaban kasa

A ranar Laraba, 17 ga watan Maris, 2021, wani kwamitin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa cancanta ce kurum za ta yi aiki a siyasar 2023 ba komai ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban wannan kwamiti da gwamna Bala Mohammed, ya jagoranta, ya na bayanin yadda za su tunkari 2023.

Gwamnan na jihar Bauchi wanda shi ne ya duba yadda aka kaya da jam’iyyar ta PDP a zaben 2019 ya ce ba yanki za a duba wajen fito da ‘dan takara ba.

Sanata Bala Mohammed ya gabatar da rahoton binciken da su ka yi gaban majalisar NWC, inda ya ce akwai bukatar a ba kowane bangare dama a 2023.

KU KARANTA: Matasa sun nemi a ba Gwamna Wike takarar shugaban kasa

Kwamitin ya ce: “Wasu su na ganin a 2023, ya kamata a kai takara zuwa Arewa maso gabas ko Kudu maso gabas ne saboda su ne ba su dade a mulki ba.”

Mohammed ya ce: “Duk da masu wannan kira su na da hujja mai karfi, ka da mu saki hanya domin mu na da ‘yan takarar da su ka cancanta a kowane yanki.”

"Saboda halin da ake ciki a yanzu, ka da a sake ayi wani rangwame wajen zabo ‘dan takarar da zai iya ceto kasar nan daga halin ka-ka-ni-ka-yin da aka shiga.”

Ya kara da: “Saboda haka mu na ganin a ba kowane ‘Dan Najeriya daga kowane yankin kasar nan dama ta hanyar shirya zaben fitar da gwani mai nagarta.”

Atiku, Kwankwaso za su iya kai labari, PDP ta fadi yadda za ta fitar da ‘Dan takarar 2023
Gwamna Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

KU KARANTA: 2023: Ministocin Tarayya da ake tunanin su na harin Gwamna

Ganin gwagwarmayar da aka yi wajen #EndSARS, wannan kwamiti ya kuma bada shawarar a ware kason wasu kujeru da mukamai ga matasa da mata.

“Wannan shi ne ra’ayinmu, hanyar da za a bi wajen cin ma nasara a zaben 2023.” Inji kwamitin.

A makon nan aka ji cewa tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya yi ganawa ta musamman da Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar.

Ayo Fayose ya zauna da tsofaffin sojojin da su ka yi mulki ne a lokacin da ya ziyarci garin Minna. Fayose ya bayyana wannan shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Tsohon Gwamnan na jihar Ekiti ya na cikin masu hangen kujerar shugaban kasa a 2023

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit Nigeria

Online view pixel