NAFDAC: Wata bakuwar cuta daga gubar abinci ta bullo a jihar Kano

NAFDAC: Wata bakuwar cuta daga gubar abinci ta bullo a jihar Kano

- Wata cuta da ake zargin wani nau'in abin sha ne ke jawo shi ya bullo a jihar Kano a Najeriya

- Hukumar NAFDAC ne ta tabbatar da barkewar cutar da ta hallaka mutane tare da jikkata da dama

- Hukumar ta bayyana cewa, tana ci gaba da binciken musabbabin cutar tare da gano asalinta

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce bakon rashin lafiya da ya bullo a Kano ya samo asali ne daga guban abinci.

Mojisola Adeyeye, darakta-janar na NAFDAC, ta tabbatar da hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda barkewar wani sabon cuta da ya haifar da mutuwar mutane biyu tare da kwantar da wasu 183 a asibiti a jihar.

Ya zuwa lokacin rahoton, ana zargin musabbabin cutar guba ne ta abinci.

KU KARANTA: Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3

NAFDAC: Wata bakuwar cuta daga gubar abinci ta bullo a jihar Kano
NAFDAC: Wata bakuwar cuta daga gubar abinci ta bullo a jihar Kano Hoto: EveryEvery NG
Asali: UGC

Ma'aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar da cewa marasa lafiyar da suka kamu da cutar sun nuna alamun cutar haematuria wanda ke haifar da fitsarin jini ko fitsari mai duhu, zazzabi, kasala, da kuma wani lokaci ciwon ciki.

Adeyeye ta bayyana lamarin a matsayin "mai tsananin gaske", ta kara da cewa har yanzu ana ci gaba da bincike.

“Lamarin na Kano lamari ne na gubar abinci tare da abubuwan sha masu kamshi wadanda ke da wani sinadari da ake kira dan sami. Yana da matukar tasiri saboda guba ne na abinci dake haifar da gudawa, amai, da kan iya kai wa ga kwanciya a asibiti.” inji ta.

“Daraktanmu na shiyya, Masanin magani Gimba, yana kan wannan lamarin kuma jami’anmu masu lura da magunguna suna binciken abin da ya faru a zahiri.

“Za mu yi gwaji mai yawa a dakin gwaje-gwaje don gano yanayin wannan sinadarin da watakila ya kai ga guban abinci.

Darakta-janar din, duk da haka, ta ce har yanzu ba ta da cikakken bayani game da asalin ababen shan da ake zargin kuma har yanzu NAFDAC ba ta gano ko ta amince da kamfanin da ke sarrafa abin shan ba.

KU KARANTA: Abdurrasheed Bawa ya bukaci ma'aikatan banki da su gaggauta bayyana kadarorinsu

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar ga jama'a.

Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.

Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel