Boko Haram sun kai hari, sun kone makaranta da dakin shan magani a Yobe

Boko Haram sun kai hari, sun kone makaranta da dakin shan magani a Yobe

- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai farmaki kauyen Katarko dake jihar Yobe da karfe 5:30 na safiyar Talata

- Sun kai harin yayin da jama'a ke sallar asubahi inda suka kone makaranta da dakin shan magani

- Mayakan sun kafa tutocinsu a sansanin sojoji kafin daga bisani su bankawa wurin wuta ya kone kurmus

Mayakan Boko Haram dauke da makamai sun shiga kauyen Katarko dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe inda suka kone wata makarantar firamare da dakin shan magani.

Lamarin ya faru da karfe 5:30 na safiyar Talata yayin da Musulmai ke sallar Asubahi.

Katarko gari ne mai nisan kilomita 18 daga Damaturu wanda ke fuskantar hare-hare masu tarin yawa har da tashin bam a wata gada da ta hada Katarko da Buni Yadi da Biu a baya.

Vanguard ta ruwaito cewa, wani mazaunin yankin mai suna Mohammed Ahmed ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun fatattaki sojoji wanda hakan yasa jama'a suka dinga neman wurin tsira.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun yi wa makiyaya 22 kisan gilla a garin Monguno dake Borno

Boko Haram sun kai hari, sun kone makaranta da dakin shan magani a Yobe
Boko Haram sun kai hari, sun kone makaranta da dakin shan magani a Yobe. Hoto daga Thecable.ng
Asali: UGC

Majiyar tace: "Mayakan Boko Haram sun shiga kauyen Katarko kuma sun kafa tutocinsu a sansanin sojoji kafin daga bisani su kone sansanin."

Kamar yadda wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanar, "Wurin karfe 5:50 na safe muka fara jin harbe-harbe daga ko ina. Tuni muka fara gudu zuwa daji domin neman tsira.

"Maharan sun bankawa makarantar firamare da cibiyar shan magani wuta kafin su isa sansanin sojoji dake Katarko su dinga harbe-harbe."

A lokacin rubuta wannan rahoton, ba a riga da an ji ta bakin jami'an tsaro ba.

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta kwatanta rahoton samar da gwamnatin gargajiya ta Biafra da Asari Dokubo yayi da wasan yara daga mutum mai bukatar jan hankalin jama'a.

A yayin jawabi ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a kan wannan cigaba a Legas ranar Litinin, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, yace hankalin shugaban kasa ba zai dauku da wannan shirmen ba.

"Idan Asari Dokubo na son kafa gwamnatin gwaji ne, zai iya yin hakan. Hankalin wannan gwamnatin ba zai dauko da shirmensa ba saboda muna da abubuwan yi."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel