Jihohin da kayan abinci suka yi tashin gwauron zabo a Nigeria

Jihohin da kayan abinci suka yi tashin gwauron zabo a Nigeria

- Hukumar NBS ta fitar da rahoto a kan yadda farashin kayan masarufi suke a kasar

- Rahoton hukumar ya nuna an samu tashin farashin kaya da kimanin kaso 17.33 cikin dari a watan da ya gabata

- A ma'aunin shekara shekara na hukumar, jihar Kogi ce ta fi tsadar farashin kayan masarufi

Rahoton da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar, ya nuna cewa akwai banbanci a hauhawan da farashin kayayyaki yayi a tsakanin jihohin kasar.

A bisa ga rahoton na hukumar NBS, an samu tashin farashin kayayyaki da kimanin kaso 17.33 cikin dari a watan Fabrairun da ya gabata.

Haka kuma tashin farashin ya karu ne da kaso 1.54 cikin 100 a cikin watan Fabrairun 2021 idan aka daura a mizani da kaso 1.49 cikin 100 da aka samu a watan Janairu.

Jihohin da kayan abinci suka yi tashin gwauron zabo a Nigeria
Jihohin da kayan abinci suka yi tashin gwauron zabo a Nigeria Hoto: Fraym
Source: UGC

Farashin kayan masarufi ya 'daga da kashi 21.79 cikin 100 a Fabrairu da ya gabata idan aka daura shi a mizani da kaso 20.57 na watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: 2023: Ana halin fargaba yayinda PDP ke shirin yanke hukunci kan yankin da za ta baiwa tikitin Shugaban kasa

Ta kuma bayyana cewa wannan shine karo na farko da aka samu irin wannan hayewar da farashi kayayyaki yayi a cikin shekaru hudu da suka gabata.

Alkaluman ya nuna farashin kayan masarufi ya 'daga sosai cikin makonni biyun da suka gabata saboda tawayen da kungiyar dillallen abinci suka yi na kin kai kayayyaki daga yankin arewa zuwa kudu.

Rahoton ya kuma nuna cewa tashin farashin ya shafi abinci irin su biredi, nama, kifi, dankali da kuma farashin kayan miya da na kayan gwari.

A ma'aunin shekara, jihar Kogi aka fi samun hauhawar farashin kayan masarufi da kaso 30.47, sai jihar Ebonyi da kashi 25.73 da kuma jihar Sokoto da kashi 25.68, BBC Hausa ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Nigeria ta ragargaji mayakan Boko Haram a wani arangama

A ma'unin wata-wata, rahoton ya ce jihar Kogi ce aka fi samun hauhawar farashin kayan abinci tsakanin Janairu zuwa Fabrairu da kaso 3.34, Ondo kaso 3.33 da Ebonyi kaso 3.26.

A wani labarin, hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce bakon rashin lafiya da ya bullo a Kano ya samo asali ne daga guban abinci.

Mojisola Adeyeye, darakta-janar na NAFDAC, ta tabbatar da hakan a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda barkewar wani sabon cuta da ya haifar da mutuwar mutane biyu tare da kwantar da wasu 183 a asibiti a jihar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng News

Online view pixel