Hana sa Hijabi: Mutum 3 sun jigata yayinda rikici ya barke tsakanin Musulmai da Kirista

Hana sa Hijabi: Mutum 3 sun jigata yayinda rikici ya barke tsakanin Musulmai da Kirista

Rikicin hana sanya Hijabi a wasu makarantu mallakin kungiyoyin addinin Kirista a jihar Kwara ta munana da safiyar Laraba yayinda Kiristoci suka nuna rashin amincewarsu da umurnin gwamnati.

A karo na biyu, gwamnatin jihar ta kulle makarantun domin kwantar da kuran.

Amma a daren Talata, kwamishanar ilimin jihar, Kemi Adeosun, ta sanar da umurnin bude makarantun.

Daily Trust tattaro cewa yayinda dalibai suka koma makaranta da safiyar Laraba, an hanasu shiga saboda Malamai kiristoci da shugabannin makarantan sun fara gudanar da zanga-zanga na nuna rashin amincewa.

An samu labarin cewa rikici ya barke a makarantar Baptist dake Surulere kafin yan kasar suka kwantar da kuran.

Har yanzu gwamnatin jihar Kwara ba tayi jawabi kan lamarin ba.

Rikicin Hijabi: Kiristoci sun rufe kofofin shiga makaranta yayinda gwamnati ta bada umurnin budesu
Rikicin Hijabi: Kiristoci sun rufe kofofin shiga makaranta yayinda gwamnati ta bada umurnin budesu Credit: @tvcnewsng
Asali: Twitter

A daren jiya, gwamnatin ta saki jawabin bada umurnin bude makarantu.

"Gwamnati ta gamsu cewa dokar da ta kafa na baiwa dalibai Musulmai daman sanya hijabansu zuwa makaranta zai tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna," cewar kwamishanar Ilimin Kwara, Kemi Adeosun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel