Yanzu-yanzu: Gwamnati ta dakatad da jiragen Azman daga tashi

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta dakatad da jiragen Azman daga tashi

- Daya daga kamfanonin jirage mallakin dan Arewa ya samu matsalolin kwanakin baya

- Hakan ya sa gwamnatin tarayya ta bukaci gudanar da bincike kan kamfanin jirgin

- Saboda haka, hukuma ta dakatad da jiragen kamfanin Azman daga tashi illa ajalin musamman

Hukumar kula da jiragen sama (NCAA) ta dakatad da jiragen kamfanin Azman Air daga tashi a Najeriya har na tsawon wani lokaci.

Hukumar ta sanar da hakan ne a jawabin da shugabanta, Musa Nuhu, ya rattafa hannu.

An yiwa jawabin take da "NCAA ta dakatad da jiragen Azman Air daga yanzu."

A jawabin, Nuhu ya bayyana cewa an dakatad da kamfanin jirgin ne domin gudanar da bincike kan kamfanin.

"Sakamakon wasu hadura da suka faru da jirgin Azmar Air Boeing 737, hukumar kula da jiragen sama NCAA.....ta dakatad da dukkan jiragen kamfanin Azman Air Boeing 737 daga tashi fari daga ranar 15 ga Maris, 2021," cewar jawabin.

"An yi wannan dakatarwan ne domin hukumar ta samu damar gudanar da bincike kan kamfanin kan ummu-haba'isin haduran dake faruwa, da kuma bada shawara domin kiyaye gaba,"

KU KARANTA: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta dakatad da jiragen Azman daga tashi
Yanzu-yanzu: Gwamnati ta dakatad da jiragen Azman daga tashi Credit: www.channelstv.com
Asali: UGC

DUBA NAN: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock

A bangare guda, ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, a ranar Litinin ya ce za a sake bude filin jirgin sama na Malam Aminu Kano don jigilar jiragen kasa da kasa a ranar 5 ga Afrilun 2021.

Ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin zaman kwamitin fadar Shugaban kasa kan annobar korona, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma ce za a sake bude filayen jiragen sama na Fatakwal da Enugu don zirga-zirgar jiragen kasa da kasa a ranar 15 ga Afrilu, 2021 da 3 ga watan Mayu, 2021.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel