Da duminsa: Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, ya yi allurar rigakafin Korona, za'a yiwa sauran Sanatoci

Da duminsa: Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, ya yi allurar rigakafin Korona, za'a yiwa sauran Sanatoci

- Yan siyasa a Najeriya ne mutanen farko da ake yiwa allurar rigakafin cutar Korona

- Shugaban majalisar dattawa ya shiga jerin wadanda sukayi rigakafin

- Gwamnatin Najeriya ta ce zata cigaba da amfani da rigakafin Astrazeneca duk da cewa ana korafi kanta

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya yi nasa allurar rigakafin Korona a ranar Talata, 16 ga watan Maris, 2021.

Hadiminsa na sabbin kafafen yada labarai, Abubakar Usman, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da hotuna.

Ahmad Lawan ya shiga jerin jami'an gwamnati da aka yi musu allurar rigakafin.

Yace: "Yanzun nan shugaban majalisar dattawa ya yi nasa allurar rigakafin Korona na Astrazeneca na farko."

Da duminsa: Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, ya yi allurar rigakafin Korona, za'a yiwa sauran Sanatoci
Da duminsa: Shugaban majalisa, Ahmad Lawan, ya yi allurar rigakafin Korona, za'a yiwa sauran Sanatoci Credit: @MrAbuSidiq
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar bude filin jirgin saman Kano

Kalli bidiyon lokacin da akayi masa:

DUBA NAN: Hankali ya tashi: An sace amarya ana saura awanni 48 a daura auren ta

A bangare guda, kasashen Turai goma sha bakwai sun dakatad da amfani da rigakafin COVID-19 na Astrazeneca har sai sun kammala bincike kan lamarin daskarewar jini a jikin wadanda sukayi.

Hukumomi a kasar Denmark ranar Alhamis sun dakatad da yiwa mutane rigakafin na tsawon makonni biyu bayan wata mata wacce aka yiwa ta samu daskarewar jini kuma ta mutu.

Najeriya dai ta ƙaddamar da fara rigakafin Astrazeneca na Korona a ranar Juma'a, 5 ga wtaan Maris 2021. Sannan a ranar Asabar aka tsirawa shugaban ƙasa da mataimakinsa rigakafin kuma annuna a kafar talabijin kai tsaye.

Gwamnatin tarayya ta ce allurar rigakafin da za'a yiwa 'yan Najeriya iri ɗaya ce da wanda akayima shugaban ƙasa manjo janar Muhammadu Buhari.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel