Ministan Buhari ya bayyana yadda tsohon Shugaban hukumar EFCC, Magu zai kare
- Abubakar Malami ya yi karin haske kan makomar tsohon shugaban EFCC, Magu
- Ministan shari’ar ya ce dokar kasa za ta yi aiki a wajen binciken Magu da ake yi
- Malami ya ki bada amsa ko gwamnati za ta shiga kotu da tsohon shugaban EFCC
Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya tabo batun tsohon shugaban hukumar EFCC da aka tsige, Ibrahim Magu.
A 2020 Abubakar Malami ya kai karar Ibrahim Magu wajen mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, wannan ya sa aka kore shi daga ofis.
Da ya yi hira da jaridar Daily Trust, Abubakar Malami ya amsa tambaya a kan makomar Ibrahim Magu.
Ministan shari’an ya bayyana cewa kotu da doka su ke da ta-cewa a kan yadda tsohon shugaban na hukumar EFCC da aka sallama, Ibrahim Magu, zai karata.
KU KARANTA: Abin da Magu ya fada mani da aka nada ni - Bawa
“Tsarin aikin ofis a kan wannan batu da lamarin da ake ciki ne zai yi tasiri a game da wannan.”
A hirar, Malami ya yi magana a game da zaben Abdulrasheed Bawa da ya yi a matsayin sabon shugaban EFCC, amma ba a ji maganar da ya yi a kan Magu ba.
Bayan makomar Magu bayan ya bar ofis, ‘yan jarida sun tambayi Ministan ko gwamnatin tarayya za ta gurfanar da tsohon shugaban na EFCC a gaban kotu.
“Ba ni da tabbas, ba zan yi azarbabi game da abin da bincike ya gano ba, domin har yanzu ana tsakar aiki ne.” Da aka tambayi Malami ko za a kai Magu kotu.
KU KARANTA: Za a bude filin tashi da saukar jiragen saman Kano
Abubakar Malami ya kare matakin da ya dauka na tura wa shugaban kasa sunan Abdulrasheed Bawa a matsayin Magajin Magu, ya ce Bawa ba ‘danuwansa ba ne.
Dazu kun ji cewa lauyoyin hukumar EFCC sun fara kiran shaidu a karar da aka kai tsohon Sanata, Shehu Sani inda ake tuhumarsa da karbar dalolin kudin Sani Dauda.
Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, kuma har an saurari hujjar wayar salula da aka yi tsakanin Alhaji Sani Dauda da tsohon Sanatan na Kaduna ta tsakiya.
An dakatar da shari’ar, Alkali ya ce za a koma a cigaba da zama a yau 16 ga watan Maris, 2021.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng