Jerin kasashe 17 da suka dakatar da amfani da rigakafin Astrazeneca, har yanzu Najeriya na amfani da ita

Jerin kasashe 17 da suka dakatar da amfani da rigakafin Astrazeneca, har yanzu Najeriya na amfani da ita

- Wata mata a kasar Austria ta mutu sakamakon daskarewar jini bayan yin rigakafin AstraZeneca

- Hukumar lura da kiwon lafiya ta musanta wani alaka tsakanin daskarewar jini da rigakafin

- Wasu kasashe akalla 17 sun bi sahun Austriya a nahiyar Turai

Kasashen Turai goma sha bakwai sun dakatad da amfani da rigakafin COVID-19 na Astrazeneca har sai sun kammala bincike kan lamarin daskarewar jini a jikin wadanda sukayi.

Hukumomi a kasar Denmark ranar Alhamis sun dakatad da yiwa mutane rigakafin na tsawon makonni biyu bayan wata mata wacce aka yiwa ta samu daskarewar jini kuma ta mutu.

An dauki "wannan mataki ne bayan jini ya daskare a jikin wasu mutane da aka yiwa rigakafin Koronan Astrazeneca," hukumar lafiyan Denmark tace a wani jawabi.

Hakazalika, kasar Norway ta dakatad da amfani da rigakafin Astrazeneca.

Ga jerin kasashen duniya 17 da suka dakatad da amfani da rigakafin kawo yanzu:

1. Andalus

2. Jamus

3. Italiya

4. Netherland

5. Cyprus

6. Ireland

7. Thailand

8. Denmark

9. Norway

10. Iceland

11. Austria

12. Bulgaria

13. Romania

14. Estonia

15. Lithuania

16. Luxembourg

17. Latvia

KU KARANTA: Jerin jihohi 16 da suka samu kasonsu na rigakafin COVID-19 da adadin da suka samu

Kasashe 7 sun dakatar da amfani da rigakafin Astrazeneca bayan wasu sun mutu, irinta Najeriya ta kawo
Kasashe 7 sun dakatar da amfani da rigakafin Astrazeneca bayan wasu sun mutu, irinta Najeriya ta kawo
Asali: Twitter

KU KARANTA: Na tattauna da Gumi, ya yi alkawarin taimaka mana wajen magance matsalar tsaro, NSA Monguno

Najeriya ta ƙaddamar da fara rigakafin Astrazeneca na Korona a ranar Juma'a. Sannan a ranar Asabar aka tsirawa shugaban ƙasa da mataimakinsa rigakafin kuma annuna a kafar talabijin kai tsaye.

Gwamnatin tarayya ta ce allurar rigakafin da za'a yiwa 'yan Najeriya iri ɗaya ce da wanda akayima shugaban ƙasa manjo janar Muhammadu Buhari.

Shugaban hukumar lafiya, Dr. Faisal Shu'aib ne ya faɗi hakan yayin taron kwamitin yaƙi da cutar corona a Abuja.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel