Mutum uku sun mutu, sama da167 na jinya a asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano

Mutum uku sun mutu, sama da167 na jinya a asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano

- Sabuwar cuta ta bulla a kananan hukumomi takwas na jihar Kano

- Kawo yanzu akalla mutum uku sun mutu a sakamakon cutar

- Gwamna Ganduje ya haramta sayar da sinadaran hada lemu a fadin jihar

Akalla mutum uku sun hallaka yayinda akalla mutum 167 ke kwance asibiti ranar Alhamis sakamakon shan lalataccen sinadarin hada lemu a jihar Kano.

Bayan shan wannan abu, wasu cikin marasa lafiya suka fara amai da ganin jiri, hakazalika wasu suka fara fitsarin jini, rahoton Daily Nigerian.

An tattaro cewa unguwannin da wannan abu ya fi shafa sun hada da Warure, Dandago da Sabon Sara.

Rahoton ya bayyana cewa a Warure Makasa, mutum 13 yan gida daya suka jigata. A Garangamawa da Sabon Sara kuwa mutum biyu sun mutu.

An tattaro cewa wannan cuta ta yadu wasu kananan hukumomin jihar.

Diraktan sashen kula da cututtuka da ma'aiktar lafiyan jihar, Dr Bashir Lawan, ya bayyana cewa hukumar ta kebance wuraren jinya takwas domin kula da masu cutar.

Ya tabbatar da cewa cutar ta yadu kimanin kananan hukumomin jihar takwas.

KU KARANTA: Gwamna Uzodimma ya sa wa titi sunan shugaba Buhari

Mutum biyu sun mutu, 167 na jinya a asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano
Mutum biyu sun mutu, 167 na jinya a asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano
Source: Original

DUBA NAN: Hotunan shugaba Buhari yayin da ya karba bakuncin shugaban kasan Nijar a Aso Rock

A bangare guda, gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar ga jama'a.

Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.

Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wadannan sinadaran da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel