Yari ga Matawalle: Kayi taka-tsan-tsan da yadda kake kula da tsaron jihar Zamfara

Yari ga Matawalle: Kayi taka-tsan-tsan da yadda kake kula da tsaron jihar Zamfara

- Tsohon gwamna Zamfara, Abdulaziz Yari ya baiwa Gwamna Bello Matawalle shawara a kan tsaron jihar

- Yari ya bukaci Matawalle da yayi taka-tsan-tsan da shawarwarin da ake bashi a fannin tsaron jiharsa

- Tsohon gwamnan ya bukaci Gwamna Bello Matawalle da ya guji siyasantar da lamarin da ya shafi rayukan jama'a

Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ja kunnen Bello Matawalle a kan siyasantar da kalubalen tsaro da ke addabar jihar.

A yayin jawabi ga manema Labarai a ranar Litinin a Talatan Mafara, Yari ya shawarci Matawalle da "yayi tunani mai zurfi a kan kowacce shawara da aka bashi wurin shawo kan matsalar tsaro."

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya bukaci Matawalle da ya hada kai da gwamnatin tarayya wurin shawo kan matsalar.

KU KARANTA: Wanne 'yan bindiga zasu dauka, jan kunne ko wa'adin da ka basu?, Dawisu ga Buhari

Yari ga Matawalle: Kayi taka-tsan-tsan da yadda kake kula da tsaron jihar Zamfara
Yari ga Matawalle: Kayi taka-tsan-tsan da yadda kake kula da tsaron jihar Zamfara. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin manoma da makiyaya: Ka gaggauta yin taron tsaron kasa, Tinubu ga Buhari

"Rashin tsaro matsala ce da ta addabi duniya, kowacce kasa tana da nata kalubalen tsaro. Amma ya dace mu hada karfi da karfe wurin tabbatar da tsaron jama'armu," yace.

"Mu kiyayi saka ra'ayi ko siyasa a duk al'amuran da ya shafi rayuwar mutane. Mun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani taro a Abuja a makon da ya gabata.

"Ba tare da duban banbancin siyasa ba, dukkanmu dake taron mun yanke shawarar aiki tare da gwamnatin tarayya wurin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa ba a Zamfara kadai ba, a kasar baki daya.

“Gwamna Matawalle yayi taka-tsantsan yayin shawo kan matsalar tsaro a jihar, yayi tunani mai zurfi a kan kowacce shawara idan aka bashi a kan kalubalen tsaron jihar."

Ya musanta zargin da ake yi na cewa 'yan jam'iyyar APC na goyon bayan 'yan bindiga dake jihar.

"A lokacin da nake gwamna, ban taba zargin jam'iyyar adawa da daukan nauyin 'yan bindiga," yace.

A wani labari na daban, fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Maulidin kasa dake jihar Sokoto sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kankara zuwa Sheme dake jihar Katsina.

Majiyoyi da dama a yankin sun sanar da cewa basu san yawan wadanda aka sace ba yayin da jami'an 'yan sanda suka ce babu wanda aka sace.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wasu majiyoyin sun ce an sace mutum 70 inda wasu suka ce fasinjoji 50 ne aka yi awon gaba dasu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng