Gwamnatin Najeriya za ta yi muhimmin zama da ‘Yan kasuwa a kan farashin litar man fetur

Gwamnatin Najeriya za ta yi muhimmin zama da ‘Yan kasuwa a kan farashin litar man fetur

- Gwamnatin Tarayya za ta yi taro da ‘yan kasuwa a kan farashin man fetur

- Shugaban kungiyar IPMAN, Mr. Chinedu Okoronkwo ne ya sanar da hakan

- Chinedu Okoronkwo yake cewa gwamnatin ta aiko masu da goron gayyata

Jaridar This Day ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta gayyaci manya da ‘yan kasuwa masu cin gashin kansu domin a zauna a game da farashin man fetur.

Gwamnati za ta zauna da ‘yan kasuwan ne ganin yadda gangar danyen mai yake tashi a Duniya.

Shugaban kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwar mai na kasa, Chinedu Okoronkwo, ya bayyana haka a lokacin da ya yi hira da gidan talabijin na Arise News jiya.

Mista Chinedu Okoronkwo ya ce gwamnati za ta cin ma matsayar da zai yi wa kowa daidai a zaman da aka shirya za ayi da manyan ‘yan kasuwan kasar.

KU KARANTA: Litar fetur zai kai N212 a gidajen mai -PPPRA ta yi karin kudi

Okoronkwo ya yi tir da hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashi bayan fitar da wata sanarwa da ba ta yi tsawon rai ba, wanda ta kai farashin lita zuwa N212.

Shugaban kungiyar na IPMAN ya ce idan gwamnati ta cire hannunta daga farashi, kamata ya yi a maida hankali kan saukin samun wannan kaya ba farashin ba.

Kawo yanzu babu wanda ya san farashin da za a koma saida fetur a kasuwa. Gwamnatin tarayya za ta yi karin farashi ne idan ta gama zama da kungiyoyin kwadago.

Mista Okoronkwo ya ke cewa ana kashe Naira biliyan 70 wajen sayen fetur a Najeriya, hakan ya na nufin duk rana ana batar da Naira biliyan biyu a man na fetur.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya na shirin yin ƙarin kuɗin dakon man fetur

Gwamnatin Najeriya za ta yi muhimmin zama da ‘Yan kasuwa a kan farashin litar man fetur
Man fetur zai iya kara tsada
Asali: Twitter

‘Dan kasuwar ya yi magana a kan kokarin da gwamnati ta ke yi na ganin an koma wa gas a madadin fetur.

Idan da za a rungumi amfani da gas, gwamnatin tarayya za ta samu sararin daukar nauyin wasu bangarori kamarsu ilmi, kiwon lafiya da ayyukan more rayuwa.

Tun kwanaki ku ka ji cewa ‘yan kasuwa su na ganin yadda kasuwar Duniya ta ke a yanzu, ya kamata farashin PMS watau man fetur ya tashi a gidajen mai.

‘Yan kasuwa sun ce ya kamata litar man fetur ya kara kudi, ya kai kamar N185 zuwa N200.

Wasu manyan kungiyoyin ‘yan kasuwa sun yi magana da 'yan jarida, inda su kace rashin karin farashin zai sa gwamnati ta dawo da biyan kudin tallafin fetur.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng