Watanni 3 da bude Jami’o’i Malaman Jami’a na barazanar komawa danyen yajin-aiki a 2021

Watanni 3 da bude Jami’o’i Malaman Jami’a na barazanar komawa danyen yajin-aiki a 2021

- Kungiyar ASUU ta ce an hana Malaman Jami’a albashi wata da watanni

- Farfesa Ayo Akinwole ya ce akwai masu bin bashin albashin watanni 10

- ASUU ta zargi Gwamnati da saba alkawuran da aka yi da ita a Disamba

A ranar Lahadi, 14 ga watan Maris, 2021, kungiyar malaman jami’a a Najeriya ta yi gargadi cewa za ta iya koma wa yajin-aiki a shekarar nan.

Jaridar The Nation ta rahoto kungiyar ASUU ta na jan-kunnen gwamnatin tarayya a kan cin zarafin ‘ya ‘yanta da kuma hana su albashinsu.

Rahoton ya ce ASUU ta zargi gwamnatin Najeriya da yin dabarar hana malaman makarantun jami’a albashinsu har na tsawon watanni 10.

A wani jawabi da ya fito ta bakin shugaban ASUU na jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ne malaman jami’ar kasar su ka bayyana wannan.

KU KARANTA: NASU da SSANU za su shiga yajin aiki a Jami'o'i

Ayo Akinwole ya ce duk da a watan Disamban 2020 su ka janye yajin-aikin da su ka yi, har yanzu su na bin bashin albashin watanni biyu zuwa 10.

Farfesan ya ce gwamnati ta taso wasu malaman jami’a a gaba saboda irin rawar da su ka taka a dogon yajin-aikin da aka yi a shekarar da ta gabata.

Kungiyar ta ke cewa duk da ta dawo bakin-aiki, matsin tattalin arziki da su ke fuskanta saboda rashin biyan albashinsu ya na jawo masu cikas.

Bayan haka, shugaban na ASUU ya ce gwamnati ba ta dawo masu da kudin kungiya da ta zara daga cikin albashin malaman jami’ar tarayya ba.

KU KARANTA: Malaman Jami’ar Maiduguri sun ce an hana su albashin watanni

Watanni 3 da bude Jami’o’i Malaman Jami’a na barazanar komawa danyen yajin-aiki a 2021
Ministan kwadago na kasa, Dr. Chris Ngige
Asali: Twitter

Farfesa Akinwole ya ce idan aka kai malaman bango, za su koma yajin-aikin da su ka baro a 2020, idan hakan ta faru, a zargi gwamnati ba kowa ba.

A lokacin da ASUU ta ce ta cika alkawari, Akinwole ya ce gwamnati ta nace a kan IPPIS, ta yi watsi da UTAS da aka kawo, ana hana su albashi.

A cikin watan Disamba bara ne gwamnatin tarayya da ASUU su ka yarda a janye yajin-aiki.

Amma duk da haka, gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi na cewa an gaza cika alkawari.

Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan Kwadago, Chris Ngige, ta yi martani game da kalaman shugaban na ASUU, ta ce an yarda a bude jami'o'in.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng