Dalla-dalla: Mutane 3 ake kashewa a Kaduna a kowanne rana cikin shekarar 2020
Rayyukan mazauna jihar Kaduna uku ke salwanta a kowanne ranar cikin kwanaki 365 na shekarar 2020 hakan ke nuna jimillar mutane 937 yan bindiga da wasu sauran miyagu suka kashe a jihar, The Cable ta ruwaito.
A ranar 20 ga watan Yulin 2020 a kauyen Kukum-Daji da ke karamar hukumar Kaura a jihar kaduna, wasu matasa bayan hallartar daurin aure suka yanke shawarar cigaba da shagulgula har cikin dare. Misalin karfe 10 na dare yan bindiga suka isa wurin da suke suke bude musu wuta suka kashe 16 nan take.
Watanni biyu a ranar 12 ga watan Satumban 2020, wasu iyali na hanyarsu ta zuwa gona a kauyen Udawa a karamar hukumar Chikun suka hadu da masu garkuwa. An sace 17 cikinsu, yayin da hudu suka tsira da rauni.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula
Wadannan kadan ne daga cikin hare-haren da yan bindiga da masu garkuwa suka kai a Kaduna a 2020.
Wasu alkalluma daga jihar Kaduna:
1. An kashe a kalla mutum daya a kowanne karamar hukuma
2. An yi garkuwa da a kalla mutum daya a kowanne karamar hukuma
3. Ba a samu satar dabbobi ba a kananan hukumomi 9
4. Kananan hukumomin da aka fi samun hare-hare sune, Giwa, Igabi, Birnin Gwari
5. An kai hare-hare a dukkan kananan hukumomi da ke jihar Kaduna
6. Karamar hukumar Igabi itace aka fi kashe mutane mafi yawa 152
KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano
7. Karamar hukumar Birnin Gwari ce aka fi garkuwa da mutane mafi yawa 519
8. Karamar hukumar Giwa ce aka fi satar dabobi inda aka sace 2,109 cikin shekarar ta 2020
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya fitar da wannan alkalluman yayin gabatar da rahoton tsaro ta shekara-shekara a farkon watan Maris.
Rahoton ya nuna cewa a kalla a kowanne rana ana garkuwa da a kalla shida a shekarar 2020, jimillar wadanda aka yi garkuwa da su a jihar 1,972.
Bisa la'akari da wannan rahoton ana iya hasashen cewa ana iya kai hare-hare a kananan hukumomin Giwa da Igabi. A farkon watan Maris, yan bindiga sun kai hari a wata makaranta da ke karamar hukumar Igabi amma jami'an tsaro sun yi nasarar ceto dalibai 172.
A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.
Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.
Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng