'Yan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula

'Yan bindiga sun kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula

- Yan bindiga sun kai wa yan sanda hari a sansanin su da ke jihar Bauchi

- Jami'i mai muƙamin sufeta da wani farar hula sun rasu sakamakon harin

- Kakakin yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin

Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari Naborodo Safer Highway Patrol na jihar Bauchi a hanyar Bauchi-Jos inda suka kashe jami'i mai muƙamin sufeta ɗan shekara 35.

Sun kuma halaka wani farar hula ɗaya yayin harin kamar yadda The Punch ta ruwaito.

'Yan bindiga kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula
'Yan bindiga kai hari sansanin ƴan sanda, sun kashe sufeta da farar hula. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dama ta samu: An sake buɗe shafin bada tallafin rancen COVID-19 daga bankin CBN

Rundunar yan sandan ta sanar da hakan ta bakin kakakinta Ahmed Wakili a ranar Lahadi.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar.

Wakil ya ce, "Rundunar yan sandan jihar Bauchi na bakin cikin sanar da cewa a ranar Asabar 14 ga watan Maris, misalin 9.30 na dare, ƴan bindiga sun kai mata hari a Naborodo Safer Highway Patrol.

"Lamarin ya yi sanadin rasuwar jami'i mai muƙamin sufeta, sufeta Mukhtar Ibrahim, 35, da wani farar hula Uba Sama'ila mazaunin garin Naborodo da harsashi ta same shi daga bisani ya rasu a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi."

KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan wasu mutane masu raƙuma da suka ɓulla a Kano

Wakil ya ce yan sanda sun gano bindigar marigayin mai lamba 32486.

Ya ce an bawa iyalan wadanda suka rasu gawarwakinsu domin yi musu jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Kakakin ƴan sandan ya ce za a tura karin jami'ai zuwa yankin.

A wani rahoton daban kun ji cewa, rundunar yan sandan jihar Kano ta kwantar da jama'a hankula game da wasu bakin mutane tare da rakuma da suka bayyana a wasu sassan jihar.

Daily Nigerian ta gano cewa mazauna jihar sun ankarar da yan sanda kan bakin mutanen da suka yada zango a wasu sassan jihar.

Wasu mazauna garin suna zargin matafiyar sun iso jihar ne domin aikata laifi da sunan fataucin kanwa.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel